Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti

Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti

- Bayan umarnin kora da gwamnan Ondo ya yi wa Fulani, sun dunguma sun koma jihar Ekiti

- Kungiyar manoma masara ajihar Ekiti sun bayyana cewa Fulanin sun fara yi musu barna

- Kungiyar ta ce Fulanin sun shiga gonar masara mai darajar miliyan 10 shanu sun cinye komai

Makiyaya sun yi kaura daga jihar Ondo zuwa jihar Ekiti, biyo bayan umarnin kora da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya yi, The Nation ta ruwaito.

Sakataren kungiyar masarufin sarrafa masara ta Najeriya, (MAGPAMAN), Mista Tope Emmanuel ne ya bayyana haka jiya a Ado-Ekiti yayin da yake zantawa da manema labarai.

Emmanuel ya ce makiyayan tare da shanunsu sun lalata gonar mambobin kungiyar ta MAGPAMAN ba tare da wani hukunci ba.

Ya kara da cewa sun mamaye gonar ne da daddare da muggan makamai don kiwon shanunsu.

KU KARANTA: Mata sun cancanci yabo ko don zaman gida da suke yi, Jarumar Nollywood

Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti
Makiyaya sun tattara nasu-ya-nasu daga jihar Ondo sun cilla Ekiti Hoto: Stears Business
Asali: UGC

Emmanuel ya ce manoman da abin ya shafa sun samu kusan rancen Naira miliyan 6.6 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) a karkashin shirin masu karbar bashi don shuka masara, yana mai cewa sun tafka asara ta kimanin Naira miliyan 10.

“Shekarar da ta gabata, mun tuntubi CBN a matsayin kungiya don neman rancen da ya kai Naira miliyan 6.6 don gonar masara kuma mun shuka masara da ta kai hekta 235 na gonar, muna tsammanin kimanin Naira miliyan 10 a matsayin riba." in ji shi.

Emmanuel ya bukaci Gwamna Kayode Fayemi da sauran masu ruwa da tsaki da su cece su daga makiyayan.

Ya ce ‘yan sanda, 'yan bangan Amotekun da sauran jami’an tsaro na sane da faruwar lamarin, amma ba su sa baki ba saboda dalilan da su suka fi sani.

Kwamandan Amotekun Brig.-Gen. Joe Komolafe, wanda ya tabbatar da ci gaban, ya ce: "" Muna kan halin da ake ciki. "

KU KARANTA: Amurka ta ginawa Najeriya asibiti mai darajar $1.3m don kebe masu COVID-19

A wani labarin, Sarakunan gargajiya a jihar Ondo a ranar Alhamis sun bayyana cewa Fulani kamar kowane kabila suna da 'yanci su zauna tare da gudanar da ayyukansu na halal a koina a cikin kasar nan ciki har da jihar Ondo, The Nation ta ruwaito.

Sarakunan gargajiyan da suka bayyana goyon baya kan umarnin da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya bayar kan makiyaya su fice daga dazukun gwamnati a cikin kwanaki bakwai ya ce dole ne Fulani su mutunta haƙƙin dukiyar mutane.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.