Miyetti Allah K/Hore: Da Buhari ya na son mu, da gwamnati tayi wa Makiyaya wuraren kiwo
- Miyetti Allah Kautal Hore tace ta fi jin dadi kafin zuwan Gwamnati mai-ci
- Kungiyar ta karyata rade-radin cewa Muhammadu Buhari yana ba su fifiko
- Shugaban Miyetti Allah yace Makiyaya ba su amfana da mulkin Buhari ba
Sakataren kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na kasa, Saleh Alhassan, ya ce ana maida makiyaya saniyar ware a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Alhaji Saleh Alhassan ya bayyana haka ne a lokacin da jaridar Punch ta yi hira da shi a karshe makon da ya wuce.
Saleh Alhassan yake cewa abin da mutane suke tunani na cewa fadar shugaban kasa ta na ba Makiyaya fifiko da kariya a Najeriya, sam ba daidai ba ne.
“Kuskuren da mutane su keyi shi ne, suna taso Makiyaya a gaba da cewa shugaban kasa (Muhammad Buhari) ya na basu wata kariya.” Inji Alhassan.
KU KARANTA: Miyetti Allah ta ba gwamnatin tarayya shawara
Jagoran na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ya ce: “Buhari bai da wata dangantaka da Makiyaya. Wannan ita ce gaskiya.”
“Idan mutane suka ce shi ne uban kungiyarmu, shin Jonathan da ya fito daga Kudu maso kudancin Najeriya, bai zama uban kungiyarmu ba? Alhassan ya tambaya.
Alhassan ya cigaba: “Don Shugaban kasa ya na Fulani, babu ta inda wannan ya taimaki rayuwar Makiyayi. Asali ma, mun fi jin dadi kafin Buhari ya karbi mulki.”
“Mai ake amfana da shi. Ba su cin moriyar gwamnati, amma (Makiyaya) ne su ke samar da tulin naman da ake ci a Najeriya.”
KU KARANTA: Makiyaya: Gwamna ya bada umurnin daukan 'Yan Amotekun
Ya ce: “Buhari bai yi mana komai ba sai jawo mana makiya. An taso makiyaya a gaba. Da ace Buhari yana sonmu, da ya samar mana da wuraren kiwo.”
A makon da ya wuce kun ji cewa Mai ba Buhari shawara, Bashir Ahmaad ya yi wa Atiku Abubakar shagube bayan ya roki shugaban kasa Joe Biden alfarma.
Ahmaad ya kunsawa tsohon Mataimakin Shugaba kasa Atiku magana a kaikaice ne a Twitter.
Wannan lamari ya jawo surutu, inda magoya bayan 'dan adawar suka dura kan hadimin na shugaban kasa Muhammadu Buhari, su ka ce ana zargin gwaninsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng