Garambawul a Gwamnatin Kano: Gwamnan Abba Yusuf Ya Yi Sababbin Nade Nade 19

Garambawul a Gwamnatin Kano: Gwamnan Abba Yusuf Ya Yi Sababbin Nade Nade 19

  • Gwamnatin Kano ta amince da naɗin sababbin sakatarorin dindindin 19 tare da sauya wa 14 da ke kan aiki ma’aikatu domin ƙarfafa gudanarwar gwamnati
  • Shugabar ma’aikatan jihar ta ce naɗin ya zo ne domin inganta aiki, ƙarfafa shugabanci da tabbatar da kyakkyawan ba da hidima ga al’ummar Kano
  • Sababbin naɗe-naɗen sun fara aiki nan take, yayin da aka umarci dukkan waɗanda abin ya shafa su kammala miƙa aiki kafin ranar 12 ga watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta amince da sabon zagayen naɗe-naɗen manyan ma’aikatan gwamnati, inda ta naɗa sababbin sakatarorin dindindin guda 19 tare da sauya wa sakatarori 14 da ke kan aiki wuraren aiki a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban-daban.

An sanar da sauye-sauyen ne a ranar Talata cikin wata sanarwa da Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu-Maimota, ta fitar ta hannun Daraktar Wayar da Kai ta Ofishin Shugabar Ma’aikata, Rukayya Uba-Sulaiman.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana yadda gwamnatin Tinubu ta jefa 'yan Najeriya cikin wahala

Gwamna Abba Yusuf ya yi sababbin nade nade
Gwamna Abba Yusuf yana duba wasu takardu a ofishinsa na gwamnan Kano. Hoto: @Kyusufabba
Source: Facebook

Gwamnati ta bayyana dalilin naɗe-naɗen

Sanarwar ta bayyana cewa sabbin naɗe-naɗen da sauye-sauyen an yi su ne domin ƙara wa waɗanda abin ya shafa nauyin jagoranci tare da ƙarfafa tsarin aikin gwamnati da inganta gudanar da mulki a faɗin jihar Kano.

Ta ƙara da cewa ana sa ran sababbin sakatarorin dindindin da waɗanda aka mayar zuwa wasu ma’aikatu za su yi aiki kafada da kafada da shugabannin ma’aikatunsu domin ciyar da shirye-shiryen ci gaban gwamnatin jihar gaba da kuma inganta ba da hidima ga jama'a.

Haka kuma, an buƙaci dukkan jami’an da aka naɗa ko aka sauya musu wurin aiki su gudanar da ayyukansu cikin ƙwazo, ƙwarewa, gaskiya da riƙon amana.

An umarci jami'ai su fara aiki nan take

Hajiya Bilkisu Shehu-Maimota ta bayyana ƙwarin gwiwarta cewa sabbin sakatarorin dindindin za su cika abin da ake sa ran za su yi, tare da ci gaba da kare martaba da ƙa’idojin aikin gwamnati na jihar Kano ta hanyar nuna ƙwarewa, gaskiya da sabbin dabarun gudanarwa.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta dakatar da wani babban biki a Yobe, an cafke ɗan TikTok a Kano

A cewarta, wannan naɗi kira ne zuwa ga ƙarin nauyi da hidima ta gaskiya ga al’ummar jihar Kano.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa dukkan naɗe-naɗen da sauye-sauyen sun fara aiki nan take, yayin da aka umarci dukkan jami’an da abin ya shafa su kammala dukkan matakan miƙa da karɓar aiki kafin ranar 12 ga watan Agusta.

Nasarar Abba kan kiwon lafiya

Wannan ci gaban ya biyo bayan wasu muhimman ayyukan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar a fannin lafiya, ciki har da buɗe Cibiyar Kula da Masu Cutar Sikila da kuma sabon ginin Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KCDC).

Gwamnatin Kano ta yi sauye sauye a wasu muhimman ma'aikatu
Taswirar jihar Kano, inda Gwamna Abba Yusuf ya nada sababbin manyan sakatarori. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Gwamnan ya kuma ƙaddamar da rabon na’urorin auna hawan jini guda 300 ga ma’aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa, tare da fara rabon kayan kula da mata masu juna biyu, kayan sashen gaggawa da sabbin zanen gadon asibitoci a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano.

Yusuf ya ce waɗannan shirye-shirye na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin inganta harkokin kiwon lafiya da kuma ƙarfafa tsarin kula da lafiyar al’ummar jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rikici ya danno cikin kungiyar goyon bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027

An sauya sunan ma'aikata a Kano

A wani labari, kun ji cewa gwamnan Kano ya amince da canza sunan Ma'aikatar Mata, Yara da Nakasassu zuwa Ma'aikatar Mata, Yara da Masu Bukata ta musamman.

Kwamishina a Ma'aikatar da aka canza sunan, Hajiya Amina Sani Abdullahi ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a Kano.

Hajiya Amina ta bayyana yadda Gwamna Abba ya damu da masu bikata ta musamman, in da ta ce yana yawan tambayar halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com