An Bayyana Lokacin da Israila Za Ta Janye Sojojinta daga Gaza

An Bayyana Lokacin da Israila Za Ta Janye Sojojinta daga Gaza

  • Hukumar Board of Peace ta ce Isra’ila za ta janye daga Gaza ne bayan an kammala kwace makaman Hamas
  • Daraktan hukumar, Nickolay Mladenov, ya gana da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026
  • Kungiyar Hamas mai fafutukar kwatar 'yancin Falasdinawa ta ce ba za a aiwatar da yarjejeniyar ba sai Isra’ila ta cika nata bangaren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Gaza - Hukumar Board of Peace karkashin jagorancin Amurka ta ce janyewar sojojin Isra’ila daga Zirin Gaza ba za ta faru ba sai bayan an kammala kwace makaman Hamas.

Hukumar ta bayyana hakan ne bayan ganawar da daraktanta, Nickolay Mladenov, ya yi da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

Ana so Israila ta janye sojojinta daga Gaza
Firaministan Israila, Benjamin Netanyahu Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce ganawar ta gudana ne a ranar Litinin a Yammacin birnin Kudus, yayin da wasu ’yan siyasar Isra’ila suka nuna rashin gamsuwa da yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Pantami na shirin sanin makomarsa, PDP ta samu koma baya a Gombe

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da yarjejeniyar a ranar Alhamis da ta gabata.

An bayyana sharadin janyewar Isra’ila

Board of Peace ta ce makasudin yarjejeniyar a bayyane yake, wato kwace dukkan makaman da ke Gaza da kuma kawo karshen mulkin amfani da makami domin a koma tsarin mulkin farar hula.

Hukumar ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa a kafar sada zumunta bayan ganawar.

A cewar hukumar, shirin ya hada da kwace kananan makamai da manyan makamai tare da rufe hanyoyin karkashin kasa da ake amfani da su.

Ana amfani da sunan “Yellow Line” wajen bayyana layin da aka ware, wanda sojojin Isra’ila ke ci gaba da zama a bayansa a Gaza.

Hamas ta kafa nata sharadin

A nata bangaren, Hamas ta ce ba za a aiwatar da yarjejeniyar ba sai Isra’ila ta fara cika nata bangaren na yarjejeniyar.

A yayin tattaunawar, Mladenov ya bukaci Netanyahu ya dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza, kamar yadda wasu mutane biyu da suka san abin da aka tattauna suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP).

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake kunyata Trump a idon duniya

Sai dai Isra’ila ta ki amincewa da dakatar da hare-haren duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi a watan Oktoban 2025.

Rahoton ya ce tun bayan yarjejeniyar tsagaita wutar, Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 1,200, ciki har da fiye da 36 bayan sanar da yarjejeniyar kwace makaman.

An kuma ce sama da Falasdinawa 73,000 ne suka mutu a Gaza tun bayan fara yakin Isra’ila a watan Oktoban 2023.

Netanyahu ya nuna rashin gamsuwa

Kafin ganawar, ofishin Netanyahu ya ce tsarin yarjejeniyar da aka bayyana a bainar jama’a bai nuna matsayar Isra’ila ba. Ofishin ya ce Isra’ila ta riga ta bayyana damuwarta ga gwamnatin Amurka.

Wasu mambobin gwamnatin Netanyahu masu tsattsauran ra’ayi sun nuna cewa suna son a sake duba yarjejeniyar.

Ministan kudi, Bezalel Smotrich, ya ce yarjejeniyar ta sha bamban da wadda gwamnatin Isra’ila ta amince da ita. Ya bukaci a sake kada kuri’a kan yarjejeniyar nan take.

Sojojin Israila za su bar zirin Gaza
Wasi sojojin Israila a Kudancin Lebanon Hoto: @idfonline
Source: Twitter

Sojojin Israila sun yi bore

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sojoji da dama daga Bataliyar Tzabar ta rundunar Givati sun bar sansaninsu da ke kudancin Isra’ila bayan rikici da kwamandansu.

Rundunar IDF ta ce sojojin sun fice daga sansanin Sde Teiman ba tare da amincewar manyansu ba, inda suka bar makamansu a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng