'Dan TikTok a Najeriya Ya Jefa Shugaban 'Yan Sanda a Matsala, an Fara Bincike

'Dan TikTok a Najeriya Ya Jefa Shugaban 'Yan Sanda a Matsala, an Fara Bincike

  • Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa tana binciken AIG Moshood Jimoh kan zarge-zargen da VeryDarkMan ya yi
  • Rundunar ta ce an gayyaci AIG Jimoh domin yi masa tambayoyi a wani binciken cikin gida da take gudanarwa
  • Haka kuma, ‘yan sanda sun gayyaci VeryDarkMan domin ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zarge-zargensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

FCT, Abuja - Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa tana binciken Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (AIG), Moshood Jimoh, mai kula da shiyyar Zone 2.

Rundunar ta ce an gayyace shi ne kan zarge-zargen da fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta, Martins Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan, ya yi.

An gayyaci mataimakin sufeton 'yan sanda
Mataimakin sufeto janar na 'yan sanda da Verydackman Hoto: Verydackblackman
Source: Facebook

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Ani Iniedu, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

An gano bayanai kan ƙirƙirar hukumar PFIPC bayan an kammala binciken ICPC

Rundunar ta ce an gayyaci AIG Moshood Jimoh domin yi masa tambayoyi a matsayin wani bangare na binciken gudanarwa na cikin gida.

Sai dai ta bayyana cewa shari’ar da ta shafi zarge-zargen tana gaban kotu mai hurumin sauraron karar.

Haka kuma, rundunar ta ce ta gayyaci Martins Otse domin ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da ikirarin da ya yi.

Abin da ‘yan sanda suka ce

Sanarwar ta ce:

“Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta lura da kalamai da bayanan da Mista Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), ya yi a bainar jama’a da kuma kafafen sada zumunta dangane da Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda mai kula da Zone 2 da ke Legas, da kuma wata shari’ar da ke gudana.”
“Rundunar na son bayyana hakikanin bayanai tare da fayyace matsayin hanyoyin shari’a da binciken gudanarwa da ake bi.”

Rundunar ta ce an gudanar da bincike kan shari’ar da aka ambata a bayanan jama’a, kuma yanzu tana gaban kotu mai hurumin sauraron karar.

Kara karanta wannan

Faston da ya buga da Tinubu a fadar shugaban kasa ya sake magana

A cewar sanarwar, an kai karar kotu ne bayan samun shawarar Sashen Gurfanar da Jama’a (DPP).

Shari’ar tana gaban kotu

Rundunar ta ce tun da shari’ar tana gaban kotu, alhakin yanke hukunci ya rataya ne kacokan a kan bangaren shari’a.

Ta jaddada cewa ba za ta yi shari’ar a kafafen yada labarai ba, kuma ba za ta bari yakin neman goyon bayan jama’a ko sharhi su yi tasiri a kan yadda za a yanke hukunci ba.

Sanarwar ta ce:

“Rundunar ba za ta gudanar da wannan shari’a a kafafen yada labarai ba, kuma ba za ta bari sakamakonta ya kasance karkashin tasirin yakin neman goyon bayan jama’a ko kalaman da ke kokarin yanke wa jami’ai ko bangarorin da abin ya shafa hukunci tun kafin kotu ta yanke nata hukuncin ba.”

An gayyaci AIG Moshood Jimoh

Rundunar ta ce tana gudanar da binciken cikin gida bisa tsarin da take da shi na tabbatar da rikon amana.

Ta tabbatar da cewa Mataimakin Sufeto Janar mai kula da Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda (Force CID) ya gayyaci AIG Moshood Jimoh domin yi masa tambayoyi kan zarge-zargen da aka gabatar.

Kara karanta wannan

An tsinci gawar malami a yashe, an ce wasu ne suka daɓa masa wuka har lahira

An gayyaci VeryDarkMan Abuja

Sanarwar ta ce rundunar ta kuma gayyaci Martins Otse domin ya tabbatar da zarge-zargen da ya yi.

A cewarta, Force CID da ke Abuja ta aika wa Otse da gayyata a hukumance ranar 30 ga watan Yuli, 2026, domin ya bayyana a ofishinta da ke Abuja.

'Yan samda sun gayyaci Verydarkman
Dan gwagwarmaya a kafafen sada zumunta, Verydarkman Hoto: Verydackblackman
Source: Facebook

An kashe jami'in dan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da wani hari da ’yan kungiyar Lakurawa suka kai garin Girkau da ke karamar hukumar Kebbe.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’in dan sanda da fararen hula biyu, yayin da wasu mutane suka samu raunuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com