Makinde: ‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane ne makiyanmu ba Makiyaya ba

Makinde: ‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane ne makiyanmu ba Makiyaya ba

- Gwamnan Oyo ya fito ya soki matakin Takwaransa na haramtawa Makiyaya kiwo

- Seyi Makinde ba ya goyon bayan korar Makiyaya daga jejin Jihohin da suke zama

- Gwamnan yake cewa hakan ya sabawa dokar kasa da ta ba kowa ‘yancin balaguro

Gwamna Seyi Makinde ya ce makiyan al’umma sune miyagun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, ba makiyaya masu neman abincin dabbobi ba.

Jaridar The Cable ta ce gwamnan jihar Oyo ya bayyana wannan ne a ranar Laraba, 20 ga watan Junairu, 2021, a wani jawabi da ya yi wa mutanensa.

A jawabin na sa na jiya, gwamnan ya ce sam ba zai goyi bayan wani daga cikin mutanen Oyo ya kai wa mazauna jiharsa hari ko da wani irin suna ba.

Seyi Makinde, ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta yi na’am da wa’adin da wasu kungiyoyi ko daidaikun mutane suke ba jama’a cewa su bar jihar Oyo ba.

KU KARANTA: Yaro ya yi garkuwa da ubansa, ya karbi miliyoyi

A cewar gwamnan yin hakan ya ci karo da dokar da ta ba ‘yan kasa damar shiga ko ina a Najeriya.

“Ba za mu yi watsi da cewa ana samun aukuwar abubuwan da ya kamata a duba ba. Zaman lafiyan makiyaya da manoma a oke Ogun na fuskantar barazana.”

“Tsirarun mutane da ba hukuma ba, suna yawo, suna korar jama'a daga gidajensu, suna kawo hatsaniya. Wannan farmaki ba shi ne zai kai yarbawa ga ci ba.”

“Bari in bayyana cewa ba za mu zauna, muna kallo a maida masu bin doka su zama cikin dar-dar a gidajensu ko gonaki ko wurin kasuwancinsu ba.” inji gwamnan.

Makinde: ‘Yan bindiga, masu garkuwa da mutane ne makiyanmu ba Makiyaya ba
Gwamna Seyi Makinde Hoto: Twitter Daga: @SeyiMakinde
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ba za a bude Makarantu a Kaduna ba - Gwamnati

Gwamna Makinde ya ce zai yi duk abin da ya dace na ganin an samu zaman lafiya a Oyo, tare da kawo karshen ‘yan bindiga da sauran makiyan da ke ta’adi a jihar.

A jihar Ondo kuwa kun ji cewa gwamnatin Rotimi Akeredolu ta ce nan da mako daya, makiyaya su fice daga jejin jihar, su nemi rajista kafin su iya ci da dabbobinsu.

Gwamnan jihar Ondo ya tsaurara matakai ne domin yaki da garkuwa da mutane da ake yi.

Gwamnan ya haramta kiwo da zarar yamma ta yi, sannan an hana hawa manyan tituna daga ranar Litinin. Haka zalika an hana kananan yara fita da dabbobi kiwo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel