Labaran kasashen waje
A labarin nan, za a ji cewa kasar Iran ta sake jaddada matsayarta a kan batun kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya yayin da ake sa ran sulhu da Amurka.
Gwamnatin Burundi ta tabbatar da rasuwar ministan sadarwar kasar a wani hadarin mota. An ce an samu gawar Gabby Bugagaan masa rauni a kayi a cikin mota.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa Iran ta sauka daga matsayarta, ta yarda ba za ta kera makamin nukiliya ba, ya ce za a koma tattaunawa.
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya yi ikirarin vewa hare-haren Amurka sun raunata jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei kuma suna zargin ya nakasa.
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa dakarunta sun shirya tsaf domin ci gaba da kai farmaki kasar Musulunci ta Iran idan har hanyar diflomasiyya ba ta cimma nasara ba.
Shugaban kasar Lebanon ya ƙi amince wa da tayin tattaunawa da Netanyahu, inda ya ce babu tattaunawa har sai an tsagaita buɗe wuta tsakanin kasashen biyu.
Kasar Amurka ta fitar da danyen mai adadin mai yawa da ba a taba gani ba tun yakin duniya na biyu saboda yakin da ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Hukumar IMF na shirin bai wa Najeriya da wasu ƙasashe tallafin $50bn domin rage raɗadin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya haddasa. An gargadi Najeriya kan ciwo bashi.
Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa ta ba da shawarar yadda za a yi da sindarin Uranium da Iran ta mallaka amma Amurka ta nuna ba haka ba, ta ce a shirye take ta koma.
Labaran kasashen waje
Samu kari