Jami'an Tsaro Sun Kama Fitaccen Limamin Masallaci da Ke Sukar Gwamnati a Burkina Faso
- Jami’an tsaro sun cafke fitaccen limamin Sunni a Burkina Faso, Mohamad Ishaq Kindo bayan ya soki wata dokar addini da gwamnati ta kafa
- An ce an kama limamin ne cikin tashin hankali a Ouagadougou yayin da mabiyansa suka yi yunkurin hana jami’an tsaron tafiya da shi
- Daruruwan mutane sun fito zanga-zanga suna neman a saki limamin, amma jami’an tsaro sun tarwatsa su da barkonon tsohuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Burkina Faso - Jami’an tsaro a Burkina Faso sun cafke fitaccen limamin Sunni kuma malamin addini mai wa’azi, Mohamad Ishaq Kindo, bayan ya soki wata dokar da gwamnati ta kafa kan harkokin addini.
Rahotanni sun ce an kama limamin ne ranar Talata a birnin Ouagadougou kafin a tafi da shi zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Source: Twitter
An kama limami kan sukar gwamnati
Kungiyar haɗin kan ƙungiyoyin Musulunci ta Burkina Faso (FAIB) ta tabbatar da kama limamin a wata sanarwa da ta fitar, kamar yadda RFI ta ruwaito.
Kungiyar FAIB ta ce har yanzu hukumomi ba su bayyana dalilin kama shi a hukumance ba.
Kafin kama shi, wani karatun limamin ya bazu sosai a kafafen sada zumunta inda yake sukar dokar da gwamnati ta kafa a watan Maris kan yadda ake gudanar da harkokin addini.
Limamin ya bukaci shugabanni su sake nazarin matakan da suke dauka kafin aiwatar da su.
A cikin karatun, malamin ya ce:
“Kowa ya yi hattara kada a hana gudanar da addu’o’i a wuraren taruwar jama’a. Ko kai shugaba ne ko mai iko, ba ka da karfi da ikon Allah.”
An samu tashin hankali yayin kamen
Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne da misalin karfe 2:00 na rana ta hannun jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji masu rufe fuska.
Wani na kusa da limamin ya bayyana cewa an samu tashin hankali yayin da mabiyansa suka yi kokarin hana jami’an tsaro tafiya da shi.
Majiyar ta ce wasu daga cikin masu ibada sun samu raunuka a yayin artabun, kamar yadda rahoton Seneweb ya nuna.
Bayan kama limamin, daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a Ouagadougou suna neman a sake shi. Sai dai rahotanni sun ce jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa.
Gwamnatin mulkin soja na fuskantar suka
Burkina Faso na karkashin mulkin soja tun bayan da Kyaftin Ibrahim Traoré ya karbi mulki kusan shekaru hudu da suka gabata.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin na ci gaba da daukar tsauraran matakai kan duk masu sukar mulkinta.
Hukumomin kasar na danganta wannan mataki da yakin da suke yi da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka addabi yankuna da dama na kasar tsawon shekaru.
Asali: Legit.ng

