Fitaccen Dan Kwallo Ya Yanke Jiki Ya Fadi a cikin Fili Ana tsakiyar Buga Wasa

Fitaccen Dan Kwallo Ya Yanke Jiki Ya Fadi a cikin Fili Ana tsakiyar Buga Wasa

  • Fitaccen dan wasan Denmark, Christian Eriksen ya yanke jiki ya fadi a fili yayin da ake tsakiyar wasan sada zumunci da Ukraine
  • Lamarin ya tayar da hankula saboda irin abin da ya faru da shi a Euro 2020 lokacin da ya samu bugun zuciya a tsakiyar fili
  • Likitan tawagar Denmark ya tabbatar da cewa na’urar da ke jikinsa ta yi aiki yadda ya kamata kuma yanzu yana cikin yanayi mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ukraine - 'Dan wasan tsakiyar Denmark, Christian Eriksen, ya razana duniya bayan ya yanke jiki ya fadi a fili yayin wasan sada zumunci tsakanin kasarsa da Ukraine ranar Lahadi.

Lamarin ya faru ne a minti na 65 yayin da Denmark ke kan gaba da ci 2-1, abin da ya sa jami’an wasa suka dakatar da wasan nan take domin ba shi kulawar gaggawa.

Kara karanta wannan

Amurka za ta saka wa kasashen Larabawa da kadarorin Iran da ta kwace a yaki

Dan wasan Denmark, Christian Eriksen, ya suma ana tsakiyar wasa
'Yan wasa da jami'ai sun yi rumfa wa dan wasan Denmark, Christian Eriksen da ya suma a tsakiyar fili. Hoto: Bo Amstrup / Ritzau Scanpix / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

'Dan wasa ya suma a tsakiyar fili

Duk da fargabar da aka samu, Eriksen mai shekaru 34 ya samu damar fita daga fili da kafafunsa ba tare da taimako ba bayan ya farfado, in ji rahoton Sky Sports.

Wannan lamarin ya sake tunatar da mutane abin da ya taba faruwa da Eriksen a gasar Euro 2020 lokacin da ya suma a wasansu da Finland saboda bugun zuciya.

A lokacin likitoci sun yi masa CPR domin ceto rayuwarsa kafin daga bisani ya murmure gaba daya. Bayan wannan matsala, an sanya masa wata na’ura ta musamman mai taimaka wa zuciya wacce ake kira ICD.

Likita ya ba da karin bayani

Likitan tawagar Denmark, Morten Boesen, wanda aka ce ya taimaka wajen ceton rayuwar Eriksen a shekarar 2021, ya tabbatar da cewa dan wasan yana cikin yanayi mai kyau.

Aljazeera ta ruwaito Boesen ya ce:

“Christian yana cikin koshin lafiya kuma ya fita daga fili da kansa. Daga yadda na gani, na’urar da ke jikinsa ta yi aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Ni ne gatansa': Trump ya fusata kan cewa Netanyahu ne ya jawo shi cikin yaki da Iran

“Ya dan suma na wani lokaci kadan amma cikin sauri ya dawo cikin hayyacinsa kuma muka samu damar magana da shi.”

Likitan ya kara da cewa an garzaya da Eriksen asibiti domin ci gaba da bincike kan musabbabin abin da ya faru.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan wasan Denmark da Ukraine sun yi gaggawar zagaye Eriksen yayin da likitoci ke kula da shi domin kare martabarsa lokacin da ya fadi.

Christian Eriksen na Denmark ya suma ana tsakiyar buga wasa
Christian Eriksen na Denmark yana karbar wata kyauta da aka bashi bayan kammala wasan sada zumunci da Ukraine a Odense. Hoto: Vitalii Kliuiev/Getty Images
Source: Getty Images

Abubuwan sani game da Eriksen

Bayan matsalar zuciyar da ya samu a 2021, Eriksen ya bar Inter Milan saboda dokokin Italiya ba sa bai wa ‘yan wasa masu ICD damar buga wasa.

Daga baya ya koma Brentford a Ingila a shekarar 2022 kafin ya koma Manchester United. Ya buga wasanni 107 a United inda ya ci kwallaye takwas tare da lashe kofin Carabao a 2023 da kofin FA a 2024.

A yanzu haka Eriksen na taka leda a kungiyar Wolfsburg ta kasar Jamus bayan ya bar Manchester United a 2025.

Dan kwallo ya mutu a tsakiyar wasa

Kara karanta wannan

Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon dan kungiyar Jigawa United, Hadi Bala Ado, ya yanke jiki ya fadi yayin da ake wasa tsakanin kungiyarsa, CD Madridejo FC da SP Cabanillas.

An rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Janairun shekarar 2023 lokacin da suke buga wasan cin kofin Spain Terceira.

An ce tawagar ma'aikatan lafiya da ke filin wasan Municipal Toledo sun garzaya don kai masa dauki, amma ba su yi nasarar farfado da shi ba, inda ya mutu nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com