Gwamna Ya Bayyana Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Jefa 'Yan Najeriya cikin Wahala

Gwamna Ya Bayyana Yadda Gwamnatin Tinubu Ta Jefa 'Yan Najeriya cikin Wahala

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce cire tallafin man fetur da barin darajar naira ta riƙa sauyawa lokaci guda sun ƙara tsananta rayuwa ga ‘yan Najeriya
  • Makinde ya ce babu ƙasar da za ta iya jure irin waɗannan manyan sauye-sauyen tattalin arziki biyu a lokaci guda ba tare da matakan rage radadin tasirinsu ba
  • Jam’iyyar APM ta ce za ta haɗa kai da jama’a domin kawo sauyi a Najeriya tare da ƙarfafa tattalin arziki da tsaro a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Abeokuta, jihar Ogun - Gwamnan jihar Oyo kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Allied People’s Movement (APM), Seyi Makinde, ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Gwamna Makinde ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da barin darajar naira ta riƙa sauyawa a lokaci guda sun jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi da 'yan bindiga suka nemi N80m bayan sace basarake

Makinde ya soki gwamnatin Tinubu
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Makinde ya bayyana haka ne ta hannun wani jagoran jam’iyyar na ƙasa, Mista Babatunde Tijani, a ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026 a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, cewar rahoton jaridar The Punch.

An yi taron ne domin ƙaddamar da ‘yar takarar mataimakiyar gwamnan APM a jihar, Misis Deborah Akinlade, da kuma ‘yan takarar majalisar dokokin jiha da na majalisar tarayya gabanin zaɓen 2027.

Makinde ya soki manufofin APC

Gwamnan ya ce babu wata ƙasa da za ta iya jure girgizar tattalin arziki biyu da gwamnatin APC ta kawo ba tare da ɗaukar matakan rage radadin tasirinsu ba.

“Ta yaya mutum zai yanke hukunci a rana ɗaya cewa zai cire tallafin man fetur ba tare da samar da wani mataki na rage radadi ko tallafin da zai cike gibin ba? A lokaci guda kuma, sai suka ci gaba da barin darajar naira ta riƙa sauyawa.”
“Waɗannan manufofi biyu sun ƙara jefa rayuwar ‘yan Najeriya cikin wahala. Babu wata ƙasa, hatta ƙasashen da suka ci gaba, da za ta iya aiwatar da irin waɗannan manufofin tattalin arziki a lokaci guda.”

Kara karanta wannan

Rikici ya danno cikin kungiyar goyon bayan Obi da Kwankwaso gabanin 2027

- Gwamna Seyi Makinde

Makinde ya kuma nuna damuwa kan yadda tsadar rayuwa ke ƙaruwa da sauye-sauyen da ake samu a kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

“Yanzu mutane nawa ne za su iya cin abinci sau uku a rana? Nawa ne farashin man fetur a baya, kuma nawa ne yanzu? Sun ce sun daidaita farashin canji, amma daga nawa zuwa nawa? Farashin zai haura zuwa N1,500, daga baya ya dawo N1,300, sannan su riƙa tafa wa kansu. Wane irin abu ne wannan?”

- Gwamna Seyi Makinde

Makinde ya yi magana kan tsaro

Da yake kwatanta halin tsaro na yanzu da na shekarun baya, Makinde ya ce tabarbarewar tsaro ta sa ‘yan Najeriya ba sa iya yin barci cikin kwanciyar hankali, TheCable ta kawo labarin.

Ya ce manufar taron ita ce a haɗa kan jama’a domin su fahimci cewa jam’iyyar APM ta samu gindin zama a jihar Ogun.

“Mun umarci mutanenmu da ke ƙasa su fara gagarumin gangami a ƙananan hukumomi da mazabu domin sanar da jama’a cewa suna cikin sabuwar jam’iyya da za ta kuɓutar da ‘yan Najeriya daga wahala da ƙuncin da ba dole ba.” Inji shi.

Kara karanta wannan

Bayan shan suka Gwamna Abba ya kare matakin ba 'yan APC filaye sama da 1500

Makinde ya ce APM ta shirya rage wahalhalun da talakawa ke ciki tare da sake fasalin Najeriya ta fuskar tattalin arziki da tsaro.

Gwamna Makinde ya soki Tinubu
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Source: Twitter

Gwamna Makinde ya mika mulki ga mataimakinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar Dokokin Jihar Oyo ta amince da bukatar Gwamna Seyi Makinde na tafiya hutun shekara.

A yayin hutun, mataimakin gwamnan jihar, Bayo Lawal, ne zai kula da harkokin mulki da gudanar da ayyukan gwamnati har zuwa lokacin da gwamnan zai dawo bakin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng