An Samu Matsala a Shirin Gwamnati na Kwaso 'Yan Najeriya daga Afrika Ta Kudu

An Samu Matsala a Shirin Gwamnati na Kwaso 'Yan Najeriya daga Afrika Ta Kudu

  • Gwamnatin tarayya ta dage jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu zuwa ranar Laraba saboda matsalolin shirye-shirye
  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da jirage biyar na Air Peace domin kwaso ‘yan Najeriya da suka nuna sha’awar dawowa gida
  • Sama da mutum 1,000 sun nuna sha’awar dawowa Najeriya daga Afrika ta Kudu yayin da aka riga aka tantance mutum fiye da 500

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da dage jigilar rukunin farko na ‘yan kasar da ke son komawa gida daga Afirka ta Kudu sakamakon hare-haren kyamar baki da suka sake barkewa a kasar.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Shugaba a majalisa ya faɗi lokacin da za a amince da dokar ƴan sandan jihohi

Najeriya ta fara shirin kwaso 'yan kasarta daga Afrika ta Kudu
Wasu daga cikin 'yan Najeriya da aka kwaso daga Afrika ta Kudu saboda hare-haren kyamar baki a 2019. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Tinubu ya amince a kwaso 'yan Najeriya

A cewarsa, an dage jigilar da aka shirya yi ranar Litinin zuwa ranar Laraba saboda wasu matsalolin shirye-shirye da suka taso, in ji rahoton Premium Times.

Ebienfa ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da amfani da jirage biyar domin kwaso ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kud .

Ya bayyana cewa kamfanin Air Peace ne zai gudanar da jigilar mutanen daga kudancin nahiyar Afrikan.

A cewarsa, jirgin farko zai tashi daga Johannesburg zuwa Najeriya da yammacin ranar Laraba bayan kammala cika dukkan wasu matakai da takardun da ake bukata.

An ce jirgin zai dauko kimanin mutum 270 daga cikin wadanda suka nuna sha’awar komawa gida.

An tantance sama da 'yan Najeriya 500

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa an tsawaita aikin tantance ‘yan Najeriya da ke son dawowa gida zuwa ranar Laraba.

Ebienfa ya ce an riga an kammala tantance sama da mutum 500 a ofishin jakadancin Najeriya da ke Pretoria.

Kara karanta wannan

Amurka ta gamu da matsala, jirgin yakinta ya rikito a kusa da mashigar Hormuz

Ya yaba da yadda aikin ke tafiya cikin lumana da tsari duk da yanayin tashin hankali da damuwar da hare-haren suka haddasa.

Ya kara da cewa mukaddashin babban jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Ambasada Olatunde Ajayi, ne ke jagorantar aikin.

Ghana ma ta kwaso ‘yan kasarta

Rahotanni sun nuna cewa ba Najeriya ce kadai ke kokarin ceto ‘yan kasarta daga Afirka ta Kudu ba, kamar yadda rahoton The Guardian ya nuna.

An bayyana cewa kasar Ghana ta riga ta kwaso sama da mutum 300 daga cikin ‘yan kasarta tun bayan barkewar sababbin hare-haren kyamar baki fiye da wata guda da ya gabata.

Hare-haren dai sun haddasa fargaba a tsakanin bakin haure daga kasashen Afirka da ke rayuwa a Afirka ta Kudu.

Dabiri-Erewa ta yi karin bayani game da 'yan Najeriya masu son barin Afrika ta Kudu
Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa tana jawabi a wani taro. Hoto: @nidcom_gov
Source: Twitter

Mutum 1,000 suna son dawowa gida

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na NAN, shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana cewa sama da mutum 1,000 sun nuna sha'awar dawowa Najeriya.

Ta ce ana gudanar da aikin tantance mutanen ne a tsarin hadin gwiwa tsakanin ofishin jakadancin Najeriya da ma’aikatar harkokin cikin gida ta Afirka ta Kudu.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya

Sababbin hare-hare da ake kai wa bakin haure a Afirka ta Kudu sun sake tayar da hankali a tsakanin kasashen Afirka.

Masu sharhi sun bayyana cewa hare-haren sun fi shafar ‘yan kasashen Afrika musamman ‘yan Najeriya, Ghana da sauran kasashen yammacin Afirka da ke zaune a kasar.

Halin da ake ciki a Afrika ta Kudu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu, sun yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin kare su daga hare-haren ƙyamar baki.

Hukumar NiDCOM ta ba wa 'yan Najeriya shawarar rufe shagunansu tsakanin 27 zuwa 29 ga watan Afrilu domin kauce wa hare-hare a lardin Gauteng.

Yayin da Najeriya ta ba da shawarar ɓuya kawai, ƙasar Ghana ta ɗauki mataki mai tsauri a lokacin da aka ci zarafin wani dan kasarta a Afrika ta Kudu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com