Dangote, Rupert da 'Yan Afirka 5 da Suka Shiga Jerin Attajiran Duniya a 2026
Kano - Alhaji Aliko Dangote ya sake jagorantar jerin masu kudin Afrika bakwai da suka samu shiga sahun mutane 500 da suka fi kowa dukiya a duniya a shekarar 2026.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kasar Amurka ce take da kaso mafi yawa a cikin jerin attajirai 500 da suka fi kowa kudi a duniya a 2026, yayin da nahiyar Afirka ke da mutum bakwai kawai da suka samu shiga jerin.

Source: Getty Images
Jerin mutum 7 mafi kudi a Afrika
Babbar mujallar nan ta Bloomberg ce ta fitar da wannan jeri a watan Mayu kamar yadda ta saba fitar da jerin attajiran duniya din a kowace shekara, bayan nazarin dukiyar da kowanne mutum ya mallaka.
A cikin wannan maƙala, mun zaƙulo attajira Afirka bakwai da suka samu shiga cikin jerin masu kudin duniya 500, da kuma taƙaitaccen tarihin su da ta dukiyar da suka mallaka.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta sa baki kan harin sojojin sama da ya kashe farar hula a Zamfara
1. Aliko Dangote ($34.9bn)

Source: Getty Images
Gwarzon ɗan kasuwar nan ɗan asalin jihar Kano, Aliko Dangote, ya zama mutum na 67 a jerin masu kudin duniya da dukiyar da aka ƙiyasta ta kai dala biliyan 34.9.
Nasarar Dangote ta ginu ne a kan rukunin masana'antunsa da ke birnin Legas, waɗanda suka mamaye harkar siminti, sukari, da gishiri a Afrika. Kazalika, matatar mai da ya ƙaddamar a 2024 ta ƙara ba shi ƙarfin gwiwa a fannin makamashi.
Dangote ya tashi ne a hannun kakansa Alhassan Dantata bayan ya rasa mahaifinsa tun yana ɗan shekara takwas, inda ya koyi dabarun kasuwanci tun yana yaro.
2. John Rupert ($18.9bn)

Source: Getty Images
Daga ƙasar Afrika ta Kudu, John Rupert ya shiga jerin masu kudin duniya a matsayi na 144 da dukiyar da ta kai dala biliyan 18.9.
Ya mallaki kamfanin Cie Financiere Richemont da ke Switzerland, wanda ya shahara wajen ƙera manyan agoguna irin su Cartier, in ji rahoton Forbes.
John Rupert, wanda yanzu ke da shekara 75, ya gaji dabarun tara dukiya ne daga mahaifinsa Anto Rupert, kuma babban kasuwancinsa na kamfanin Remgro ya ƙara faɗaɗa arzikinsa a fannin sufuri.
3. Abdussamad Isiyaka Rabiu ($18.5bn)

Source: Twitter
Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdussamad Rabiu, shi ne ɗan Najeriya na biyu da ya shiga jerin attajiran duniya 500, inda yake a matsayi na 152, da dukiyar dala biliyan 18.5.
Kamfanin simintin BUA ya samu ribar naira tiriyan 1.2 a shekarar 2025, yayin da harkar samar da taliya ta rukunin BUA ke sahun gaba a ƙasar.
Abdussamad ya tashi ne a gidan shahararren ɗan kasuwan nan Isyaka Rabiu na jihar Kano, wanda hakan ya ba shi damar kafa tasa daular a fannin gine-gine da masana'antun abinci.
4. Nathan 'Natie' Kirsh ($15.3bn)

Source: Twitter
Natie Kirsh, wanda ke da dukiyar da darajarta ta kai dala biliyan 15.3, ya yi fice ne wajen samar da abinci ta hanyar kamfaninsa na Jetro Restaurant Depot LLC wanda ke da rassa a jihohin Amurka 35.
An haife shi a 1932 a Afrika ta Kudu, inda ya fara cin gashin kansa yana ɗan shekara 26 bayan ya kammala jami'a. Tarihinsa ya nuna cewa ya fice daga kasuwancin gidansu ne domin kafa nashi kasuwancin a ƙasashen ƙetare.
5. Nicky Oppenheimer ($14.8bn)

Source: Getty Images
Nicholas Frank Oppenheimer yana matsayi na 211 a masu kudin duniya da jarin dala biliyan 14.8, kuma shi ne na biyar a attajiran Afrika.
Ya kasance babban mai hannun jari a kamfanin haƙar zinare da lu'u-lu'u na De Beers. Ya samu ɗumbin dukiyarsa ne bayan ya sayar da kashi 40 na hannun jarin kamfanin ga Anglo American a 2012.
Tarihin arzikin nasu ya samo asali ne tun daga kakansa Ernest Oppenheimer wanda ya kafa kamfanin haƙar ma'adinai a 1917, kamar yadda aka wallafa a WikiData.
6. Naguib Sawiris ($11.7bn)

Source: Getty Images
Daga ƙasar Masar, Naguib Sawiris ya samu shiga gurbin masu kudin duniya 500 da jarin dala biliyan 11.7, kuma shi ne na shida a Afrika.
Ya tara dukiya mai yawa sakamakon sayar da hannun jarin kamfaninsa na sadarwa na Vimpelcom, in ji rahoton BBC.
Naguib ya fito ne daga gidan Yousiriyya Onsi Sawiris, tsohon ɗan kwangilar da ya gina manyan hanyoyin ruwa da gadoji a yankin Kogin Nilu tun a 1950, wanda hakan ya ba shi dama ya mallaki kadarori a sassan duniya.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari
7. Nassef Sawiris ($10.1bn)
Mutum na bakwai a jerin masu kudin Afrika shi ne Nassef Sawiris, ƙaramin kani ga Naguib, wanda ke da jarin dala biliyan 10.1.
Nassef ya zaɓi ya raba kafa da kasuwancin gidansu na gine-gine, inda ya mayar da hankali kan harkar takin zamani ta hanyar kamfanin OCI a Netherlands, in ji rahoton Billionaires Africa.
Haka kuma, yana da hannun jari na 7% a kamfanin takalman wasanni na Adidas, wanda hakan ya tabbatar masa da gurbin zama ɗaya daga cikin zaƙakuran nahiyar.
Dangote zai gina sabuwar matatar mai
A wani labari, mun ruwaito cewa, Aliko Dangote ya bayyana birnin Mombasa na kasar Kenya a matsayin inda ya fi sha’awar gina sabuwar matatar mai.
Aikin wanda zai lakume dala biliyan 17, zai tace danyen mai daga Uganda da sauran sassan duniya don amfanin Gabashin Afirka.
Akwai takaddamar diflomasiyya tsakanin Kenya da Tanzania game da inda ya kamata Dangote ya gina wannan katafariyar matatar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

