"Za Su Hana Tinubu Ya Zarce a 2027," An Fallasa Shirin Amurka da Wasu Kasashen Waje
- Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa manyan ƙasashe kamar Amurka da Birtaniya za su goyi bayan jam'iyyun hamayya a zaɓen 2027
- Ya bayyana cewa kodayake Shugaba Bola Tinubu yana da dukkan dabarun lashe zaɓe, cikas ɗinsa mafi girma zai fito ne daga ƙasashen waje
- Shugaban cocin INRI Evengelical Spiritual ya gargaɗi jam'iyyun hamayya cewa muddin suka raba kansu, ba za su taɓa iya kayar da Tinubu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya sake fitowa da wasu sababbin hasashen siyasa game da makomar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da hadiminsa na yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu, Ayodele ya bayyana cewa wasu ƙasashen waje ba za su goyi bayan tazarcen shugaban ƙasar ba.

Source: Twitter
Kasashen waje za su hana Tinubu tazace
Kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito, Osho Oluwatosin ya rahoto Primate Ayodele ya na cewa:
“Kasashen waje za su goyi bayan takarar Tinubu a 2027 ba. Shugaban yana da duk abin da ake buƙata don cin nasara, amma ƙasashen waje za su kasance babban cikas ga nasararsa.
"Wasu ƙasashe da suka haɗa da Amurka, Birtaniya, da ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), sun shirya haɗa kai da jam'iyyun hamayya don ganin Tinubu ya sauka daga mulki.”
Ƙalubale ga jam'iyyun hamayya
Baya ga maganar ƙasashen waje, Ayodele ya aika da saƙon gargaɗi ga jam'iyyun hamayya na Najeriya.
Ya bayyana cewa duk wanda yake son kayar da Tinubu dole ne ya kasance mai tsattsauran ra'ayin lashe zabe domin shugaban ba zai ɗauki abin da wasa ba.
Ya jaddada cewa Tinubu a shirye yake ya yi duk abin da ya dace don ganin ya sake komawa kan karagar mulki, kuma ba zai sassauta wa duk wanda ya nuna adawa da shi ba.
Ayodele ya ƙara da cewa:
“Tinubu ya shirya yin komai don cin nasara a zaɓen. Wannan zaben ba irin na baya ba ne, domin ya riga ya kuduri aniyar yaƙar duk wanda yake son ba shi matsala a zaben. Dole jam'iyyun hamayya su shirya sosai."

Source: Facebook
Matsalar da 'yan adawa za su samu
Wani babban bangare a cikin hasashen na Primate Ayodele shi ne batun haɗin kan jam'iyyun hamayya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Babban malamin addinin ya nanata cewa muddin jam'iyyun hamayya suka ce za su shiga zaɓen 2027 a rarrabe, to gara su manta da maganar cin nasara.
A cewarsa, haɗin kai shi ne kaɗai zai ba 'yan adawa damar lallasa Shugaba Tinubu da APC, yana mai cewa:
"Idan har da gaske suke son ganin canji a mulkin ƙasar, to dole ne su ajiye son zuciya su fuskanci zaɓe a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya."
"Ba tabbas" Ayodele kan tazarcen Tinubu

Kara karanta wannan
RHA ta kafa hujjoji, ta ce Shugaba Tinubu ya cika alkawuran da ya daukar wa 'yan Arewa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Jagoran cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi gargaɗi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Primate Ayodele ya gargadi Tinubu da kada ya saki jiki game da burinsa na tazarce a wa’adi na biyu, domin har yanzu nasarar tasa ba ta tabbata ba.
Malamin ya ce har yanzu wa’adi na biyu na Tinubu bai da tabbas, kuma na kusa da shi sun rufe masa idanu ta hanyar sihiri domin hana shi ganin ƙalubalen da ke gabansa.
Asali: Legit.ng

