Asirin Amurka Ya Tonu, an Fadi Yadda Makamanta ke Karewa a Yaki da Iran
- Wani sabon rahoto ya bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da kusan kashi 80% na makaman THAAD masu kare hare-haren makamai masu linzami
- Rahoton ya ce manyan kwamandojin soja sun gargadi gwamnatin Donald Trump cewa rumbun ajiyar makaman ƙasar na raguwa sosai
- Wasu rahotanni sun ce ana zargin wannan ne ya sa aka dakatar da shirin kai sabbin hare-hare kan Iran a ƙarshen makon da ya gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma ƙwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC, Amurka – Wani sabon rahoto ya bayyana cewa sojojin Amurka sun yi amfani da mafi yawan makaman kariya daga hare-haren makamai masu linzami tun bayan fara rikicin da Iran.
An ce kusan 80% na makaman tsarin kare sararin samaniya na THAAD da kuma kusan rabin makaman Patriot sun ragu idan aka kwatanta da adadin da Amurka ke da su kafin rikicin ya fara.

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa wasu majiyoyi sun bayyana cewa manyan hafsoshin soja sun gargadi Pentagon cewa rumbun ajiyar makaman ƙasar na kara raguwa cikin matuƙar haɗari.
An gargadi Trump kan ƙarancin makamai
Rahoton ya ce ƙarancin makaman ya zama babban abin damuwa yayin da gwamnatin shugaba Donald Trump ke duba yiwuwar ƙara kai hare-hare kan Iran.
Majiyoyin sun ce ƙasashen Larabawan Tekun Fasha ma sun nuna damuwa cewa idan Iran ta kai farmaki, ƙarancin waɗannan makamai zai rage ƙarfin kare kansu.
An kuma bayyana cewa sojojin Amurka sun kusan ƙare amfani da wasu manyan makamai masu dogon zango da ake amfani da su wajen kare hare-haren makamai masu linzami.
Rahoton Times of Israel ya bayyana cewa karancin makaman zai iya yin tasiri wajen dakatar da kai hare-hare ga Iran domin gudun mai zai biyo baya.
Dalilin dakatar da sabon hari kan Iran
Rahoton ya ce kafin ƙarshen makon da ya gabata, Trump ya amince da shirin kai sababbbin manyan hare-hare kan Iran, har ma Ministan Tsaro, Pete Hegseth, ya samu umarnin fara shirye-shiryen karshe.
Sai dai daga baya aka aka ce an dakatar da shirin bayan jami'an soja sun yi gargadi kan ƙarancin makamai, tare da wasu rahotannin sirri da suka nuna yiwuwar mummunan sakamako idan aka kai harin.

Source: Getty Images
An kuma ce damuwar ƙasashen yankin Gulf game da yiwuwar ramuwar gayya daga Iran ta taka rawa wajen sauya shawarar gwamnatin Amurka.
Zuwa yanzu dai babu wai tabbaci na kawo karshen yakin a cikin kwanaki masu zuwa duk da cewa Amurka ta ce ana tattaunawa da juna.
Amurka na neman sababbin dabarun yaki
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya ta nemi jami'anta su gabatar da sababbin dabaru na musamman domin ƙara matsa wa Iran lamba.
Rahotanni sun ce wannan matakin ya biyo bayan yadda gwamnatin Donald Trump ke fuskantar ƙalubale wajen cimma burinta a rikicin da Iran.
Majiyoyi sun bayyana cewa rundunar CENTCOM ta fara nazarin sababbin hanyoyin da za ta bi domin sake fasalin dabarunta kan Iran.
Asali: Legit.ng

