Abu Ya Girma: Shugaban Kasa Ya Rushe Gwamnatin Senegal, Ya Sallami Firaminista
- Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sallami Firaminista Ousmane Sonko tare da rusa gwamnatin kasar baki daya
- Rikicin siyasa tsakanin Faye da Sonko ya kara kamari yayin da Senegal ke fama da matsin tattalin arziki da bashin asusun lamuni na IMF
- Yayin da Sonko ya yi martani, ana fargabar matakin Faye na iya janyo tsaiko a tattaunawar Senegal da asusun IMF kan bashin $1.8bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Senegal - Bassirou Diomaye Faye, shugaban kasar Senegal ya sallami Firaminista Ousmane Sonko tare da rusa gwamnatin kasar baki daya bayan watanni ana rikici tsakanin shugabannin biyu.
Sanarwar da aka karanta ta gidan talabijin na gwamnati ta tabbatar da cewa an sallami dukkan ministocin gwamnatin, amma an ce za su ci gaba da ayyukan yau da kullum har sai an kafa sabuwar gwamnati.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

Source: Twitter
Sakataren fadar shugaban kasa, Oumar Samba Ba, ne ya bayyana hakan, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ta'azzarar rikici tsakanin Faye da Sonko
Rahotanni sun nuna cewa matakin ya biyo bayan watanni ana samun rashin jituwa tsakanin Faye da Sonko, wadanda suka kasance abokan siyasa kafin daga bisani dangantakarsu ta yi tsami.
Sonko, wanda ya yi fice musamman a tsakanin matasa, shi ne ya mara wa Faye baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2024 bayan an hana shi tsayawa takara saboda hukuncin bata suna da kotu ta yanke masa.
Bayan sanar da sallamarsa, Sonko ya yi martani a shafinsa na X, inda ya wallafa cewa:
“Godiya ta tabbata ga Allah. Yau zan yi bacci cikin nutsuwa da sanyayyar zuciya a unguwar Keur Gorgui.”
Senegal na fama da matsin tattalin arziki
Rikicin siyasar na zuwa ne a lokacin da Senegal ke fuskantar matsin tattalin arziki mai tsanani, kamar yadda rahoton RFI ya nuna.

Kara karanta wannan
ADC: Atiku ya gurfana gaban kwamitin tantancewa, ya gabatar da muhimman manufofinsa
Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya dakatar da shirin bayar da lamunin dala biliyan 1.8 ga kasar bayan gano cewa an bayar da bayanan bashi da ba su dace ba.
Rahotanni sun nuna cewa bashin Senegal ya kai kashi 132 cikin 100 na karfin tattalin arzikinta zuwa karshen shekarar 2024.
Masana na ganin matakin da Faye ya dauka zai iya kara jinkirta cimma yarjejeniya tsakanin Senegal da IMF.

Source: Twitter
An samu sabani kan karin farashin mai
Kafin sallamar Sonko, ministan kudi na kasar, Cheikh Diba, ya shaida wa majalisa cewa Senegal na sa ran komawa tattaunawa da IMF a ranar 8 ga watan Yuni.
Sai dai ya bayyana cewa kudin tallafin man fetur na kasar na iya haura kasafin kudin shekarar 2026 idan farashin gangar danyen mai ya kai dala 115.
Diba ya ce Sonko ya ki amincewa da bukatar da ya gabatar na kara farashin man fetur.
Rahotanni sun nuna cewa Sonko ya yi adawa da duk wani tsarin sake fasalin bashin kasar da IMF ke son a aiwatar, yayin da aka kiyasta bashin Senegal ya kai kusan dala biliyan 13.

Kara karanta wannan
Mutane sun barke da dariya da Jonathan ya kira Sarkin Kano Sanusi II da wani suna a taro
Faye ya kafa tarihi a Senegal
A wani labari, mun ruwaito cewa, yayin da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Senegal, ɗan shekara 44, Bassirou Faye ya kafa tarihi a siyasar Afrika.
Bassirou Diomaye Faye, ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a nahiyar Afirka, bayan ya doke ‘yan takara 19 ciki har da Amadou Ba.
An ce miliyoyin mutane ne suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar Senegal na biyar bayan shafe shekaru uku ana rikicin siyasa da ba a taba ganin irinsa ba.
Asali: Legit.ng