Ana cikin Yaki da Iran, Amurka Ta Kirkiro Wata Doka da Za Ta Shafi Yan Najeriya da Wasu Kasashe
- Amurka ta bullo da sabuwar doka domin rage cunkoson bukatun neman mafaka daga yan Najeriya da wasu kasashen duniya
- Sabuwar da dokar ta bai wa hukumar USCIS damar tura bukatun kai tsaye ga alkalan shige da ficen Amurka ba tare da yin hira da mai nema ba
- Gwamnati ta ce matakin zai hanzarta yanke hukunci kan bukatun neman mafaka, tana mai cewa sabuwar dokar ta fara aiki nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Gwamnatin Amurka ta sanar da wata sabuwar doka kan masu neman mafaka a kasar, wacce za ta shafi yan Najeriya da sauran kasashen duniya.
Amurka ta ce dokar za ta ba da damar tura bukatun neman mafaka ga alkalan hukumar kula da shige da fice ba tare da masu neman mafakar sun fara halartar hira ba.

Source: Getty Images
Vanguard ta rahoto cewa Hukumar Kula da Ayyukan 'Yan Kasa da Shige da Fice ta Amurka (USCIS) ce ta sanar da sauyin, bayan wata sanarwa daga Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida (DHS).
Dalilin Amurka na kafa sabuwar doka
A tsarin da ake amfani da shi a baya, USCIS ce ke kula da bukatun neman mafaka da mutanen da ba su cikin shari'ar korarsu daga kasar ke gabatarwa.
Sai kuma alkalan shige da fice na Ma'aikatar Shari'a (DOJ) da ke sauraron bukatun wadanda ke cikin shari'ar kora daga kasar.
Dangane da matsayin mutumin da ke neman mafaka, USCIS na iya yanke hukunci kan bukatar neman mafaka ko kuma ta tura ta ga alkalin shige da fice domin ci gaba da sauraro.
Sabuwar dokar ta bai wa USCIS damar tura irin wadannan bukatu kai tsaye ga alkali ba tare da yin hira da mai neman mafakar ba.
Gwamnatin Amurka ta ce ana cin zarafin tsarin
DHS ta ce matakin zai rage lokacin da jami'an USCIS da alkalao ke dauka wajen duba bukatu, tare da taimakawa rage tarin shari'o'in da suka yi yawa a kotunan Amurka.
Daraktan USCIS, Joseph Edlow, ya ce wasu mutane sun dade suna amfani da tsarin neman mafaka domin jinkirta shari'o'i ko samun izinin aiki, maimakon neman kariya ta gaskiya.
"Tsarin neman mafaka na Amurka an kirkire shi ne domin kare mutanen da ke fuskantar tsoron tsangwama na gaskiya, ba domin a yi amfani da shi wajen neman anfani ta wata hanya ba," in ji Edlow.

Source: Getty Images
DHS ta ce jinkiri na hana aiwatar da doka
Babban Lauyan DHS, James Percival, ya ce jinkirin shari'o'i na kawo cikas ga kokarin aiwatar da dokokin shige da fice.
A cewar rahoton PM News, sabuwar dokar za ta taimaka wajen kara inganci da saurin gudanar da ayyukan hukumar.
Sabuwar dokar ta fara aiki nan take, yayin da USCIS ta bude kofar karbar ra'ayoyin jama'a kafin fitar da cikakkiyar dokar da za ta yi la'akari da shawarwarin da aka samu daga Amurkawa.
Amurka ta gargadi kasashen Afirka
An ji cewa Amurka ta ce fataucin miyagun kwayoyi da safarar mutane sun karu fiye da sau shida a Afirka cikin shekaru biyu.
Bisa haka, Amurka ta yi gargadin cewa Najeriya da sauran kasashen Afirka na fuskantar karuwar barazanar tsaro fiye da sau shida sakamakon karuwar safarar miyagun kwayoyi.
Asali: Legit.ng


