Bidiyo: Yadda Jiragen Yakin Amurka Suka Yi Karo da Juna a Sama, Suka Tarwatse
- Jiragen yakin ruwan Amurka biyu sun yi mummunan karo a sama yayin wasan kwaikwayon jirage a Idaho gaban dubban masu kallo
- Hukumomin sojin Amurka sun fara bincike domin gano musabbabin taho mu gamar jiragen da ya jawo suka tarwatse bayan faduwa kasa
- Rahoto ya bayyana halin da matukan jiragen hudu suke ciki da kuma abin da wasu ganau suka fada kan yadda mummunan lamarin ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Jiragen yakin ruwa na Amurka guda biyu sun yi karo a sararin samaniya sannan suka fadi kasa tare da tarwatsewa yayin wani wasan kwaikwayon jirage da aka gudanar a sansanin Mountain Home da ke jihar Idaho.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi yayin taron wasannin “jiragen yakin sama”, inda dubban mutane suka halarci kallon wasan kwaikwayon jiragen.

Source: Getty Images
Jiragen yakin Amurka sun yi karo da juna
Bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jiragen EA-18G Growler biyu suka yi karo a sararin sama yayin gudanar da wani wasan gudu cikin sauri, in ji rahoton The Telegraph.
Rahotanni sun ce jiragen sun fara juyawa tare a sararin sama kafin daga bisani su yi karo, sannan su rikito zuwa kasa tare da tarwatsewa, lamarin da ya haddasa wata gagarumar gobara.
Sai dai kamar yadda aka gani a bidiyon, dukkan matukan jiragen sun samu damar ficewa daga jiragen ta amfani da 'rigar iska' kafin hatsarin ya afku.
Masu kallo sun bayyana jin dadi bayan ganin rigunan iska guda hudu suna sauka daga sama bayan hatsarin.
Soke taro da martanin masu kallo
Bayan hatsarin, jami’an tsaro sun killace sansanin sojin tare da hana mutane fita yayin da jami’an kashe gobara ke kokarin shawo kan wutar da ta tashi sakamakon faduwar jiragen.
Daga bisani masu shirya taron suka sanar da soke sauran shirye-shiryen bikin na kwanaki biyu. An bayyana cewa wannan ne karo na farko da aka sake gudanar da taron tun shekarar 2018.
Wani daga cikin mahalarta taron mai suna Shane Ogden, wanda ya dauki bidiyon hatsarin, ya ce tun farko yana tunanin jiragen za su rabu kafin daga baya suka yi karo.
“Na dauka za su rabu, sai kawai na ga sun yi karo sannan suka fara juyawa tare kafin matukan suka yi anfani da rigar iska su tseratar da kansu"
- Shane Ogden.

Source: Getty Images
Gwamnatin Amurka na ci gaba da bincike
Jiragen da suka yi hatsarin mallakin rundunar Electronic Attack Squadron 129 ne da ke Whidbey Island a jihar Washington, in ji rahoton AP News.
Masana harkokin sufurin jiragen sama sun bayyana cewa irin wadannan wasannin na bukatar kwarewa sosai saboda karamin kuskure kaɗai na iya jawo hatsari.
Masani kan tsaron jiragen sama, John Cox, ya ce:
“Wasan jirage abu ne mai matukar hadari saboda babu damar yin kuskure sosai.”
Hukumomin sojin Amurka sun tabbatar da cewa an fara bincike domin gano ainihin musabbabin hatsarin.
Kalli bidiyon hatsarin da kafar watsa labarai ta Breaking 911 ta wallafa a shafinta na X:
Babban jirgin Amurka ya kama da wuta
A wani labari, mun ruwaito cewa, wata gobara ta tashi a cikin jirgin ruwan ɗaukar jiragen yaƙi na USS Gerald R. Ford (CVN-78).
Babban jirgin yana taimakawa a 'Operation Epic Fury' wanda Amurka da Isra'ila suka kaddamar ta hanyar kai hare-hare kan kasar Iran.
Hukumomi sun yi bayani game da ko tashin gobarar na da alaka da yakin da ake fafatawa, yayin da suka ce wasu sojoji sun jikkata.
Asali: Legit.ng


