Sojoji Sun Bude Kofar Karbar Tuban 'Yan Ta'adda a Dukkan Sassan Najeriya

Sojoji Sun Bude Kofar Karbar Tuban 'Yan Ta'adda a Dukkan Sassan Najeriya

  • Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da faɗaɗa tsarin karɓar miƙa wuya ga masu ɗauke da makamai zuwa Kudu maso Gabas da sauran yankunan ƙasar
  • DHQ ta ce duk masu ɗauke da makamai da suka ajiye makamansu za a karɓe su bisa dokokin ƙasa da ƙasa tare da miƙa su ga hukumomin da suka dace
  • Sojoji sun ce babu wa'adin miƙa wuya, amma sun jaddada cewa hare-haren soji kan masu aikata laifuffuka za su ci gaba da ƙaruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta sanar da faɗaɗa tsarin karɓar miƙa wuya ga masu ɗauke da makamai ba tare da izinin gwamnati ba zuwa dukkan yankunan ƙasar.

A baya dai tsarin ya fi shafar mayaƙan Boko Haram, ISWAP da ƴan bindiga da ke Arewacin Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Dara ta ci gida: Wani bam ya fashe da ƴan ƙungiyar ISWAP yayin da suke hada shi

Olufemi Oluyede da sojoji
Hafsun tsaron Najeriya, Olufemi Oluyede da wasu sojoji. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa sabon tsarin yanzu ya haɗa da masu ɗauke da makamai a Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma.

DHQ ta yi bayani kan tsarin miƙa wuya

Daraktan Yaɗa Labarai na Ayyukan Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Abuja.

Da aka tambaye shi ko an faɗaɗa tsarin zuwa sauran yankuna bayan wasu mayaƙa sun miƙa wuya ga dakarun Operation Udo Ka a Kudu maso Gabas, Onoja ya ce:

"Eh. Muna maraba da su idan suka miƙa wuya."

Ya ƙara da cewa Rundunar Sojin Najeriya za ta karɓe su bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa da Yarjejeniyar Geneva, sannan ta miƙa su ga hukumomin shari'a domin ɗaukar matakin da ya dace.

A cewarsa, rundunar soji na ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ƙa'idodin aiki, dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Majalisa ta yi sabuwar doka, za a kayyade kuɗin makarantu masu zaman kansu

Babu wa'adin miƙa wuya

Legit ta rahoto cewa Onoja ya bayyana cewa babu wani wa'adi da aka sanya wa masu ɗauke da makamai domin su miƙa wuya.

Sai dai ya jaddada cewa duk da buɗe ƙofar miƙa wuya, rundunar soji za ta ci gaba da ƙara zafafa hare-haren da take kai wa masu aikata laifuka.

Sanarwar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa hare-haren da take kai wa ƙarƙashin Operation Udo Ka sun tilasta wa wasu mayaƙa a Kudu maso Gabas miƙa makamansu.

Sojojin sun ce sun ƙwato bindigar AK-47, harsasai, bindigogi na gida da wasu makamai bayan wani da ya miƙa wuya ya jagorance su zuwa ma'ajiyar makamansu.

Dakarun sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya na gwada kayan fada. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

An kara albashin sojojin Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin albashi ga jami'an Rundunar Sojin Najeriya da ya kai tsakanin kashi 30 zuwa 80 cikin 100.

Kara karanta wannan

APC: Kwankwaso ya kwashe mutanen Abba Kabir da Ganduje zuwa NDC

Sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, 2026, inda kusan jami'ai da sojoji 250,000 za su amfana da ƙarin albashin.

Gwamnatin tarayya ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin inganta jin daɗin jami'an tsaro domin ƙarfafa su wajen yaƙi da ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng