Sun Haura $29bn: Amurka Ta Fadi Makudan Kudaden da Ta Kashe a Yaki da Iran

Sun Haura $29bn: Amurka Ta Fadi Makudan Kudaden da Ta Kashe a Yaki da Iran

  • Ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta bayyana cewa yaƙin da suke yi da ƙasar Iran ya laƙume fiye da dala biliyan 29 cikin watanni biyu kacal
  • Jules Hurst III ya bayyana cewa kuɗaɗen sun haɗa da gyare-gyare, sauya kayan yaƙi, da kuma sauran buƙatun dakarun da ke fagen fama
  • Jam'iyyar Democrat na amfani da wannan tsadar yaƙi domin sukar gwamnatin Shugaba Donald Trump gabannin zaɓen raba-gardama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Ma'aikatar tsaron Amurka (Pentagon) ta sanar da cewa yaƙin da ƙasar ke fafatawa da Iran ya lakume fiye da dala biliyan 29 a cikin watanni biyu kacal.

Wannan adadi ya nuna ƙarin dala biliyan hudu ne daga kiyasin da aka bayar a ƙarshen watan da ya gabata, wanda ke nuna yadda yaƙin ke ƙara cin kuɗaɗen haraji cikin sauri.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari

Amurka ta kashe fiye da dala biliyan 29 a yaki da Iran.
Shugaban Hafsun Sojojin Amurka, Janar Dan Caine, ya gudanar da taron manema labarai a hedikwatar tsaro ta Pentagon da ke Arlington, Virginia. Hoto: Chip Somodevilla/Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta kashe $29bn a yaki da Iran

Babban jami'in kuɗi na Pentagon, Jules Hurst III, shi ne ya tabbatar da wannan sabon lissafin kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.

Rahoton ya nuna cewa Hurst II ya fadi hakan ne yayin da yake jawabi tare da ministan tsaro Pete Hegseth da shugaban hafsun sojojin Amurka, Janar Dan Caine.

Hurst II ya bayyana cewa:

"Ya zuwa lokacin da muka bayar da shaida, mun yi maganar dala biliyan 25 ne. Amma bayan duba kiyasin da jami'anmu suka yi, muna ganin kuɗin ya kusa haura dala biliyan 29."

A cewarsa, wannan ƙari ya faru ne sakamakon buƙatar gyara da maye gurbin kayan yaƙi da suka lalace, da kuma kuɗaɗen gudanarwa na yau da kullum domin tabbatar da dakarun Amurka sun zauna daram a yankin fagen fama.

Ministan Amurka na fuskantar matsin lamba

Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth ya na fuskantar matsin lamba daga kwamitocin majalisar dokoki kan yaushe ne gwamnati za ta gabatar da cikakken lissafin kuɗin da yaƙin ke ci.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: Hotuna sun nuna yadda mutane fiye da 15 suka mutu a hanyar Kogi

Hegseth ya mayar da martani da cewa:

"Zamu bayyana abin da zamu iya, a duk lokacin da hakan ya zama wajibi."

Wannan rashi na cikakken bayani ya sa mambobin kwamitin kasafi na Majalisar Wakilai nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da dukiyar ƙasa.

Wani rahoto daga kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna cewa a watan Maris, gwamnatin Trump ta kiyasta cewa kwanaki shida na farko na yaƙin sun laƙume dala biliyan 11.3.

Wannan ya sa mutane da dama tambayar yadda Pentagon ta bi ta lissafo dala biliyan 29 a matsayin jimillar watanni biyu, duba da tsadar farkon yaƙin, in ji rahoton Irish Times.

Tasirin yakin Iran ga siyasar Amurka

Wannan dambarar na faruwa ne watanni shida kacal kafin zaɓen raba-gardama, inda jam'iyyar Republican ta Shugaba Donald Trump ke fuskantar babban ƙalubale wajen riƙe rinjayen da take da shi a Majalisar Wakilai.

Jam'iyyar Democrat na cin moriyar wannan yanayi a wurin ra'ayin jama'a, inda suke ƙoƙarin alaƙanta tsadar yaƙin da matsalolin tsadar rayuwa da suka addabi Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com