Musulma Mai Suna Rashida Ta Lashe Zabe a Kasar Amurka
- 'Yar majalisar dokokin Amurka, Rashida Tlaib, ta samu nasara a zaɓen fitar gwani na jam'iyyar Democrat a mazabar Michigan ta 12
- Tlaib ta doke abokan takararta biyu da tazarar ƙuri'u mai yawa, lamarin da ya ba ta tikitin sake neman kujerarta a babban zaɓen watan Nuwamba
- Nasarar ta zo ne bayan Tlaib ta yi fice wajen tara kuɗin yaƙin neman zaɓe fiye da sauran masu neman takarar a jam'iyyarta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Detroit, Michigan, Amurka – 'Yar majalisar dokokin Amurka 'yar asalin Falasɗinu, Rashida Tlaib, ta samu nasarar lashe zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar Democrat a mazabar Michigan ta 12.
Tlaib ta kayar da Shanelle Jackson da Byron Nolen a zaɓen da aka gudanar ranar Talata, wanda ya ba ta damar ci gaba da fafatawa domin sake komawa Majalisar Wakilan Amurka.

Source: Getty Images
Yahoo News ta rahoto cewa an ayyana Tlaib a matsayin wadda ta yi nasara tun da wuri bayan sakamakon farko ya nuna tana da gagarumar rinjaye.
Rashida Tlaib ta ci zabe
A lokacin da kamfanin dillancin labarai na Fox News ya ayyana sakamakon, an ƙirga kusan kashi 14.4% na ƙuri'un da aka kaɗa.
Tlaib ta samu ƙuri'u 13,414 daidai da 64.2%, yayin da Shanelle Jackson ta samu ƙuri'u 5,355 (25.6%) sannan Byron Nolen ya samu ƙuri'u 2,127 (10.2%).
Nasarar ta tabbatar da matsayin Tlaib a matsayin fitacciyar 'yar siyasa a jam'iyyar Democrat a jihar Michigan.
Me yasa Rashida ta yi fice?
Rahotanni sun nuna cewa Rashida Tlaib ta tara sama da dala miliyan 2.2 domin yaƙin neman zaɓenta a wannan zangon, yayin da ta mallaki kusan dala miliyan 4.7 a asusun yaƙin neman zaɓe zuwa ƙarshen watan Maris.
Masana siyasa sun bayyana cewa irin wannan ƙarfin kuɗi ya sa manyan 'yan takara suka guji kalubalantar ta a zaɓen fitar da gwanin.
Farfesan kimiyyar siyasa na Jami'ar Oakland, David Dulio, ya ce:
"Lokacin da ɗan takara yake da babban asusun kuɗin yaƙin neman zaɓe, hakan kan sa masu son kalubalantarsa su ja da baya."

Source: Getty Images
Tlaib za ta kara da ɗan Republican
Rashida Tlaib, wadda aka fara zaɓarta zuwa Majalisar Wakilan Amurka a shekarar 2018, ta shahara a faɗin ƙasar saboda ra'ayoyinta masu tsauri da kuma goyon bayanta ga manufofin masu ra'ayin sauyi.
Bayan wannan nasara, za ta kara da James Hooper na jam'iyyar Republican, wanda ya samu tikitin jam'iyyarsa ba tare da hamayya ba, a babban zaɓen ranar 3 ga watan Nuwamban 2026.
Maganar kama Netanyahu a Amurka
A wani labarin, mun ruwaito cewa magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya ce ba shi da ikon kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, idan ya ziyarci birnin.
Tun da farko Mamdani ya bayyana cewa zai kama Netanyahu saboda sammacin kotun ICC, amma daga baya ya ce ikon hakan yana hannun gwamnatin tarayya ta Amurka.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kuma bayyana cewa ba za a kama Netanyahu ba muddin yana cikin ƙasar Amurka.
Asali: Legit.ng

