Tsohuwar Gaba Ta Dawo, Wike Ya Faɗi yadda Rotimi Amarchi Ya Lalace
- Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi magana game da tasirin siyasar dan takarar mataimakin shugaban kasa, Rotimi Amaechi
- Wike ya zargi Amaechi da sauya matsaya kan zaben fidda gwani na APC, yana cewa yanzu yana cin moriyar tsarin da ya taba suka
- Ministan ya yabawa gwamnatin Tinubu kan ayyukan ci gaba a Ribas, yana cewa jihar ta samu kulawar tarayya fiye da lokutan baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayyana yadda siyasar tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, take a yanzu.
Wike ya bayyana shi a matsayin dan siyasar da ya rasa tasiri, yana mai cewa ba shi da wata kima ta zabe a Ribas da ma yankin Kudu maso Kudu.

Source: Twitter
Wike ya bayyana hakan ne yayin taron ganawarsa da manema labarai na wata-wata a Abuja, cewar Leadership.
An tambaye shi ko tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai yi la'akari da Amaechi a matsayin abokin takararsa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Ya ce idan har za a zabi Amaechi a matsayin mataimakin dan takara, ba don iya kawo kuri'u ba ne.
A cewarsa, watakila abin da ya sa aka zabe shi shi ne karfin kudi, domin ya ce tsohon gwamnan ba shi da karfin jawo nasara a zabe, ya ce tasirin siyasar Amaechi ya ragu matuka.
Ya tunatar da rawar da ya taka a yakin neman zaben Muhammadu Buhari a shekarun 2015 da 2019, da kuma goyon bayan da ya bai wa Atiku Abubakar a zaben 2023, yana tambayar dalilin da ya sa hakan bai samar da gagarumar nasara a Ribas ba.
Ministan ya ce tun bayan zaben 2011, Amaechi bai taba jagorantar wani dan takarar shugaban kasa zuwa nasara ba, ya bayyana cewa a shekarar 2011 shi ne ya kasance daraktan yakin neman zabe.
Wike ya ce ainihin jigon siyasa shi ne tsohon gwamna da har yanzu yake da goyon bayan jama'a a matakin kasa da kasa, kuma zai iya nuna ayyukan da suka amfani jiharsa da yankinsa kai tsaye.
Ya kalubalanci Amaechi da ya bayyana irin gudunmawar da ya bayar lokacin da yake kan mulki da kuma anfani da al'ummar Ribas da yankin Kudu maso Kudu suka samu daga shugabancinsa.
Haka kuma, Wike ya zargi Amaechi da rashin daidaito kan matsayinsa game da zaben fidda gwani na APC.
Ya ce Amaechi ya taba soki tsarin, yana mai cewa cike yake da kura-kurai da rashin gaskiya, amma daga baya ya amfana da wannan tsarin.
Ya ce mutum daya ne da ya taba sukar tsarin zaben fidda gwani, amma yanzu yana cin moriyar tsarin da ya kira mai cike da rashin adalci.
Wike ya kuma soki Amaechi kan matsayinsa a siyasa, ciki har da adawarsa ga sake zaben tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015 da kuma abin da ya ce rawar da ya taka wajen cire tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Justice Walter Onnoghen.
Ya tambayi ko al'ummar yankin Kudu maso Kudu za su mara wa Amaechi baya wajen cimma burinsa na siyasa a matakin kasa, idan aka yi la'akari da irin wadannan abubuwan da suka faru a baya.
Ministan ya kuma yi nuni da ayyukan more rayuwa da ake aiwatarwa a Ribas, ciki har da aikin titin Bonny Road, yana mai cewa hakan shaida ce ta yadda gwamnatin tarayya ke bai wa jihar kulawa fiye da yadda aka saba.
A cewarsa, Ribas ta samu tallafin gwamnatin tarayya da ba a taba ganin irinsa ba a karkashin gwamnatin yanzu, duk da ikirarin wasu 'yan siyasa cewa suna da kusanci da gwamnatocin baya.
Karin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng


