Iran da Amurka: An Samu Sauyin Farashin Mai a Duniya yayin da Ake Tattaunawar Sulhu

Iran da Amurka: An Samu Sauyin Farashin Mai a Duniya yayin da Ake Tattaunawar Sulhu

  • Farashin danyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 105 kan kowace ganga bayan an samu ci gaba a tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran
  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce tattaunawar na daf da kammaluwa amma har yanzu ana fargabar rikici a Gabas ta Tsakiya
  • Duk da saukar farashin mai, wasu masana sun yi gargadin cewa Brent na iya haura dala 120 idan matsalar samar da mai ta ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Farashin danyen man Brent ya sauka zuwa $105 kan kowace ganga a ranar Laraba yayin da ake ci gaba da tattaunawar sulhu domin rage rikicin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Haka kuma, farashin man WTI ya sauka zuwa $98 bayan ya yi wani tashin gwauron zabi zuwa $105 a ranar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ma'aikacin Aso Villa ya tona yadda aka shirya kutsa wa fadar shugaban kasa

An samu saukar farashin mai a duniya yayin tattaunawar Iran da Amurka.
An samu faduwar farashin mai a duniya bayan Iran da Amurka sun fara cimma matsaya a tattaunawar sulhu. Hoto: Anton Petrus
Source: Getty Images

Trump ya yi magana kan tattaunawa da Iran

Rahotanni daga shafin Oilprice.com sun nuna cewa farashin Brent ya ragu da $6 bayan ya kai $111 a ranar Talata, 19 ga Mayun 2026.

Saukar farashin man ya biyo bayan kalaman shugaban Amurka Donald Trump wanda ya ce tattaunawa da Iran ta kai matakin karshe.

Sai dai Trump ya gargadi Iran cewa za a iya ci gaba da kai hare-hare idan ba a cimma yarjejeniya ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce Iran na a shirye don hada kai da kasashen gabar teku domin samar da hanyoyin tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa.

Duk da haka, masu zuba jari da wasu masana tattalin arziki har yanzu na nuna damuwa kan yiwuwar ci gaba da tangardar samar da mai daga yankin.

An yi hasashen karin farashin mai

Wasu masana sun bayyana cewa akwai yiwuwar farashin Brent ya haura $120 kan kowace ganga nan gaba idan rikicin ya ci gaba, a cewar rahoton CNBC.

Kara karanta wannan

Ana zargin Trump da Netanyahu sun yi cacar baki game da sake kai hari kan Iran

Kamfanin Wood Mackenzie ma ya yi hasashen cewa farashin danyen mai na iya kusantar dala 200 idan mashigin Hormuz ya ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa karshen shekara.

Rahotanni sun bayyana cewa yakin da ake yi tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran tun daga ranar 28 ga Fabrairu ya yi matukar shafar zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz.

Masana na fargabar cewa farashin mai zai iya kara sama idan ba a cimma matsaya tsakanin Iran da Amurka ba
Farashin man fetur da gas a wani gidan mai a Barcelona, Catalonia, Spain. Hoto: David Zorrakino/Europa Press via Getty Images
Source: Getty Images

Rikicin Iran da Amurka ya shafi dakon mai

Kusan kaso daya cikin biyar na man fetur da makamashi na duniya ne ke bi ta wannan mashigi, kamar yadda rahoton The Guardian ya nuna.

Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jiragen dakon mai uku sun tsallaka mashigin Hormuz a ranar Laraba dauke da ganga miliyan shida na mai zuwa kasuwannin Asiya.

An kuma ruwaito cewa wani babban jirgin dakon mai mai suna Universal Winner mai dauke da ganga miliyan biyu na man Kuwait ya tsallaka mashigin bayan wasu jiragen kasar China sun fice daga yankin.

Trump ya yi barazana ga Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya ce ya dakatar da wani sabon harin soja kan Iran da aka shirya kai wa a ranar Talata.

Kara karanta wannan

"Ku tashi tsaye ku kare kan ku daga ƴan bindiga," Hadimin Tinubu ga ƴan Najeriya

Trump ya bayyana cewa shugabannin ƙasashen Qatar, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ne suka roƙe shi ya ba da damar ci gaba da tattaunawa.

Ya kuma yi gargadin cewa Amurka za ta iya kai wani mummunan hari kan Iran nan take idan ba a cimma yarjejeniyar da za ta gamsar da ita ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com