'Yan Bindiga Sun Kai Hari cikin Masallaci a Amurka, An Rasa Rayukan Bayin Allah
- Mutane uku sun mutu bayan wani harin bindiga da aka kai masallacin cibiyar addinin Musulunci ta San Diego da ke California a Amurka
- Jami’an tsaro sun ce ana binciken harin a matsayin 'harin kiyayya ga Musulmai', yayin da wadanda ake zargi biyu suka sheke kansu
- Wani jami’in tsaron masallacin mai suna Amin Abdullah ya rasa ransa yayin da yake kokarin kare jama’a daga harsasan 'yan bindigar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Mutane uku sun rasa rayukansu bayan wani mummunan harin 'yan bindiga da aka kai masallacin cibiyar addinin Musulunci ta San Diego da ke jihar California a kasar Amurka.
Jami’an tsaro sun bayyana cewa ana gudanar da bincike kan lamarin a matsayin harin kiyayya da aka kai kan al’ummar Musulmi.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun kashe mutane a masallacin Amurka

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun far wa mutane bayan sun dawo daga sayayyar kayan Sallah a Katsina
Rahotonnin jaridar The Guardian sun nuna cewa mutane biyu da ake zargi da kai harin, masu shekaru 17 da 18, sun mutu bayan sun sheke kansu.
An kai harin ne daf da lokacin gudanar da sallar azahar a masallacin cibiyar Musuluncin da ke yankin Clairemont na San Diego.
Cibiyar Musuluncin ta San Diego tana dauke da daya daga cikin manyan masallatai a yankin San Diego County.
Shugaban ‘yan sandan San Diego, Scott Wahl, ya bayyana lamarin a matsayin abin tashin hankali ga kowace al’umma.
Ya ce:
“Wannan shi ne mafi muni da kowace al’umma ke tsoro.”
Mahaifiya ta kai rahoto kafin harin
Scott Wahl ya bayyana cewa mahaifiyar daya daga cikin wadanda ake zargi ta kira ‘yan sanda sa’o’i biyu kafin harin.
Ta sanar musu cewa danta ya bace tare da wasu bindigogi da motarta. A lokacin da jami’an tsaro ke neman matasan, sai suka samu kiran gaggawa daga cibiyar Musuluncin.
Da jami’an suka isa wajen, sun tarar an kashe mutane uku ta hanyar harbin bindiga.
Jami’in tsaro ya rasa ransa
Daga cikin wadanda suka mutu akwai wani jami’in tsaron cibiyar mai suna Amin Abdullah, kamar yadda rahoton BBC ya nuna.
Wani malami, Shaykh Uthman Ibn Farooq, ya bayyana cewa Amin Abdullah mutum ne mai son kare mutane, musamman masu ibada a masallacin.
Ya ce:
“Shi dama yana da burin kare bayin Allah da ba su ji ba basu gani ba, wannan ne ma dalilin da ya sanya ya zama jami’in tsaro.”
Jami’an tsaro sun bayyana cewa jarumtakar jami’in tsaron ta taimaka wajen rage yawan barnar da harin zai iya yi.
Scott Wahl ya ce:
“Abin da ya yi ya kasance jarumtaka, kuma babu shakka ya ceci rayuka.”

Source: Getty Images
An ceto yara a makarantar cibiyar
Mahukunta sun tabbatar da cewa babu wani yaro da ya ji rauni a makarantar da ke cikin cibiyar Musuluncin.
Kafar watsa labarai ta CNN ta ruwaito cewa an samar da wurin haduwar iyalai domin taimaka wa wadanda lamarin ya shafa.
Rahotanni sun nuna cewa wani ma’aikacin gyaran lambu ma ya kusa samun rauni bayan harsashi ya bugi hular kansa.
Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka, FBI, ta ce tana tattara bayanai daga jama’a domin gano cikakken abin da ya faru.
An bude wa limami wuta a Amurka
A wani labari, mun ruwaito cewa, dan bindiga ya bude wa motar Imam Shuaib wuta a jihar Utah ta kasar Amurka a lokacin da ake gudanar da azumin Ramadan.
'Yan sanda da jami'an hukumar FBI sun fara bincike domin gano dan bindigar da kuma dalilin kai wannan hari na kisan gilla kan limamin.
Hukumar CAIR ta yi alkawarin bayar da ladar dalar Amurka 5,000 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kamo maharin.
Asali: Legit.ng

