Za a Daura Auren Donald Trump Jr., amma Shugaban Kasar Amurka ba Zai Samu zuwa ba

Za a Daura Auren Donald Trump Jr., amma Shugaban Kasar Amurka ba Zai Samu zuwa ba

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai samu damar halartar auren dansa Donald Trump Jr. ba saboda wasu muhimman dalilai
  • Donald Trump ya bayyana cewa yana son kasancewa a Fadar White House a Washington yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan rikicin Iran
  • Rahoto ya nuna cewa Donald Trump Jr. da Bettina Anderson sun riga sun yi aure a hukumance, yanzu ne za a gudanar da bikin auren a Bahamas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba zai halarci bikin auren babban dansa Donald Trump Jr. da Bettina Anderson ba.

Donald Trump ya ce ba zai halarci wannan muhimmin biki ba saboda wasu dalilai da suka shafi ayyukan gwamnatin kasar Amurka.

Shugaba Donald Trump ya ce ba zai samu damar halartar daurin auren babban d'ansa, Donald Jr. ba.
Shugaban Amurka Donald Trump da babban dansa, Donald Trump Jr. na kallon 'yan jarida a fadar White House, Washington, DC, ranar 3 ga Mayu, 2026. Hoto: Mandel NGAN / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Donald Trump ba zai je bikin babban dansa ba

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta janye kokarin tilasta wa Trump bin umarninta a yaki da Iran

Trump ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Juma’a, 22 ga watan Mayun 2025.

A cewarsa, duk da yana son kasancewa tare da dansa da sabuwar surukarsa, akwai bukatar ya ci gaba da zama a Washington DC saboda muhimman harkokin kasa.

“Duk da ina matukar son kasancewa tare da dana Don Jr. da sabuwar surukar iyalin Trump, Bettina, amma wasu dalilai da suka shafi gwamnati da kuma kaunar da nake yi wa Amurka ba za su bani damar yin hakan ba,” in ji Trump.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da bikin auren ne a karshen mako a wani karamin tsibiri da ke kasar Bahamas.

Rashin dacewar lokacin bikin ga Trump

Sai dai an bayyana cewa Donald Trump Jr. da Bettina Anderson sun riga sun yi aure a hukumance bayan samun takardar aure a Palm Beach County da ke jihar Florida.

A ranar Alhamis, Trump ya shaida wa manema labarai cewa dansa yana son ya halarci bikin, amma lokacin da aka sanya shi bai dace da tsare tsaren wasu muhimman al’amuran kasa ba.

Kara karanta wannan

Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu

Reuters ta rahoto cewa Trump ya yi karin haske, inda ya ce:

“Akwai batun da ya shafi Iran da kuma wasu muhimman abubuwa da suke bukatar hankali na a Washington DC."

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin Trump na ci gaba da tattaunawar diflomasiyya da Pakistan ke shiga tsakani domin kawo karshen rikicin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.

Rayuwar soyayya da auren Donald Jr.

Tun farko Trump ya shirya kwana a filin wasan golf dinsa da ke Bedminster a jihar New Jersey bayan wani taro a New York.

Wannan ne karo na uku da Donald Trump Jr. ya tattago batun aure.
Babban dan shugaban Amurka, Donald Trump Jr. tare da matar da ya aura Bettina Anderson. Hoto: SAUL LOEB / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai daga baya an sauya jadawalinsa domin komawarsa Fadar White House, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaran ya nuna.

Rahoton ya kuma nuna cewa wannan ne karo na uku da Donald Trump Jr., babban dan shugaban Amurka yake kinkimo aure a rayuwarsa.

Ya taba auren Vanessa, wacce suka shafe shekaru 12 tare kuma suka haifi yara biyar kafin ta nemi saki a shekarar 2018.

Daga baya ya shiga soyayya da Kimberly Guilfoyle kafin su rabu a shekarar 2024, inda daga bisani ya hadu da Bettina Anderson kuma har suka yi aure.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Ma'aikacin Aso Villa ya tona yadda aka shirya kutsa wa fadar shugaban kasa

Tsuntsu ya firgita Trump a White House

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump ya firgita yayin da wani tsuntsu ya wuce ta saman shi yana tsaka da bayani a fadar White House.

Donald Trump ya dakatar da bayanin da ya ke yi, ya koma kallon sama har ya bayyana cewa ya dauka wani jirgi maras matuki aka harbo.

Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ke takun saka da kasashen duniya da dama da suka hada da Iran, Venezuela, China da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com