Shugaban Kasar Musulunci Ta Iran Ya Yi Murabus ana cikin Yaƙi da Amurka? Gaskiya Ta Bayyana
- Fadar shugaban kasar Musulunci ta Iran ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Massoud Pezeshkian ya yi murabus daga mukaminsa
- Wani babban jami'i ya bayyana rahoton a matsayin karya tsagwaronta, inda ya zargi wasu masu tsattsauran ra'ayi da yada jita-jitar domin kawo cikas
- Fadar shugaban ƙasar ta ce ikirarin da aka danganta wa ga jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei ba shi da tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Islamic Republic of Iran - Gwamnatin kasar Musulunci ta Iran ta fito ta yi bayani yayin da aka fara yada labarin cewa shugaban kasar, Massoud Pezeshkian ya yi murabus daga mukaminsa.
Fadar shugaban ƙasar Iran ta musanta rahotannin da ke cewa Shugaba Massoud Pezeshkian ya yi murabus daga mukaminsa, tana mai bayyana labarin a matsayin "karya tsagwaronta."

Source: Getty Images
BBC Hausa ta rahoto cewa mataimakin daraktan sadarwa da yaɗa bayanai na ofishin shugaban ƙasar, Mehdi Tabatabaei, ne ya bayana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Shugaban Iran ya yi murabus?
Hadimin shugaban kasar ya ce wasu masu tsattsauran ra'ayi ne ke yaɗa irin waɗannan jita-jita domin kawo cikas ga haɗin kan jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Iran da kasar Amurka ke ƙara kamari, inda kasashen ke musayar yawu, wani lokacin su kai wa juna hare-hare.
Gwamnatin Iran ta sha nanata cewa ba ta neman yaki da kowa, amma a shirye take domin maida martani domin kare martaba da 'yancinta.
Yadda aka fara jita-jitar murabus din Pezeshkian
Rahotannin sun fara yaduwa ne bayan wasu kalamai da malamin addini, Mohammad Bagher Kharrazi, ya yi suka bazu a kafafen yaɗa labarai da na sada zumunta a Iran.
Kharrazi ya yi iƙirarin cewa jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya ce idan Shugaba Pezeshkian ya sake miƙa takardar murabus, za a amince da ita nan take.
Fadar shugaban ƙasa ta yi martani

Kara karanta wannan
Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta sake tayar da sabon tarnaki bayan ikirarin Trump
Sai dai fadar shugaban ƙasar Iran ta yi watsi da wannan iƙirari, tana mai cewa ba shi da tushe balle makama.

Source: Getty Images
Ta jaddada cewa rahotannin da ke ikirarin shugaban ƙasar ya yi murabus ba gaskiya ba ne, tare da yin kira ga jama'a da su yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa.
Ta kuma musanta kalaman da ake jinginawa Mojtaba Khamenei, tana mai bayyaja cewa ha su da tushe balle makama, kamar yadda jaridar Iran Wire ta kawo.
Iran ta lalata wasu jiragen Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta lalata jiragen yaƙin F-35 guda uku na Amurka.
Rundunar IRGC ta kuma bayyana cewa ta yi wa wasu jiragen guda uku mummunar ɓarna a wani hari da ta kai sansanin sojojin sama na al- Azraq da ke kasar Jordan.
A wata sanarwa da ta fitar, IRGC ta ce harin ya biyo bayan wani farmakin da Amurka ta kai tsibirin Qeshm, wanda ya kashe iyaye biyu da ɗansu.
Asali: Legit.ng
