Xenophobia: Najeriya da Kasashe 4 da Suka Fara Kwaso Mutanensu daga Afrika Ta Kudu

Xenophobia: Najeriya da Kasashe 4 da Suka Fara Kwaso Mutanensu daga Afrika Ta Kudu

  • Sababbin hare-haren kyamar baki a Afirka ta Kudu sun haddasa mutuwar ‘yan Afrika tare da janyo fargaba da rikicin diflomasiyya
  • Najeriya, Ghana da wasu kasashen Afrika sun fara kwaso ‘yan kasarsu daga Afirka ta Kudu saboda tashin hankalin da ake ciki
  • Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi kira da a dakatar da hare-haren tare da gargadin masu tayar da rikici a kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasashen Afrika da dama ciki har da Najeriya sun nuna damuwa kan sababbin hare-haren kyamar baki da suka sake barkewa a Afirka ta Kudu cikin makonnin baya-bayan nan.

An ce rikicin ya fara ne tun watan Afrilu, lokacin da aka ga wasu bidiyoyi da ke nuna yadda wasu ‘yan Afirka ta Kudu suke dukan ‘baki' da sanduna tare da umartar su su bar kasar.

Kara karanta wannan

Rasha, China sun yi magana bayan Iran da Amurka sun sake fara gwabza yaki

Najeriya, Ghana da wasu kasashe sun fara kwaso mutanensu daga Afrika ta Kudu
'Yan kasar Ghana sun yi cincirindo a filin jirgin sama suna jira a kwashe su daga Afrika ta Kudu zuwa gida. Hoto: Nipah Dennis / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Hare-haren kyamar baki a Afrika ta Kudu

Rahoton Premium Times ya nuna cewa zanga-zangar adawa da bakin haure da hare-haren da ake kai wa ‘yan kasashen Afrika a sassa daban-daban na kasar sun sake jawo hankalin duniya kan matsalar da ta dade tana addabar Afirka ta Kudu.

Tun a shekarar 2022, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa Afirka ta Kudu na dab da fadawa mummunan rikicin kyamar baki.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakai masu tsauri wajen yaki da wariyar launin fata da cin zarafin bakin haure.

Ana zargin wasu kungiyoyi a kasar da dora laifin matsalolin tattalin arziki, rashin aikin yi da yawaitar laifuffuka kan bakin haure daga sauran kasashen Afrika duk da cewa bincike ya musanta hakan.

Tarihin rikicin kyamar baki

Wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan rikici ke faruwa a Afirka ta Kudu ba, kamar yadda rahoton The Guardian ya nuna.

Kara karanta wannan

Yadda miji da mata suka tafka damfarar kusan N2bn da matakin da EFCC ta dauka

A shekarar 2008, an samu daya daga cikin mafi munin hare-haren kyamar baki inda aka kai wa bakin haure daga Zimbabwe, Mozambique, Malawi da Somalia hari a biranen Johannesburg, Durban da Cape Town.

A lokacin, an kashe mutane sama da 60 yayin da daruruwan mutane suka jikkata tare da tilasta wa dubban bakin haure tserewa daga gidajensu.

Rahotanni sun nuna cewa a sabon rikicin da ake fama da shi yanzu, akalla ‘yan Najeriya biyu, ‘yan Mozambique biyar da ‘yan Habasha biyar sun rasa rayukansu.

An ce wasu jami’an rundunar tsaron Afirka ta Kudu ne suka kashe ‘yan Najeriya biyun a Port Elizabeth a watan Afrilu.

Kasashen Afrika sun dauki mataki

Sakamakon rikicin, kasashe irin su Najeriya, Ghana, Kenya, Malawi, Zimbabwe da Lesotho sun gargadi ‘yan kasarsu da su yi taka-tsantsan yayin tafiya zuwa Afirka ta Kudu.

Najeriya da Ghana sun kuma gayyaci manyan jakadun Afirka ta Kudu domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda ake cin zarafin ‘yan Afrika a kasar.

Gwamnatocin kasashen Afrika sun fara kwaso 'yan kasarsu daga Afrika ta Kudu.
Wasu daga cikin 'yan Najeriya da aka kwaso daga Afrika ta Kudu saboda hare-haren kyamar baki a 2019. Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta amince da masu tada fitina ko wadanda ke daukar doka a hannunsu ba.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: NLC da TUC sun yi barazanar hana ma'aikata zuwa wurin aiki a Najeriya

Daya daga cikin manyan matakan da kasashen Afrika suka dauka shi ne fara kwaso ‘yan kasarsu daga Afirka ta Kudu.

Jerin kasashen da suka kwaso mutanensu

  1. Ghana
  2. Mozambique
  3. Malawi
  4. Zimbabwe
  5. Nigeria

Najeriya ta samu tsaikon kwaso mutanenta

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin tarayya ta dage jigilar rukunin farko na ‘yan Najeriya daga Afirka ta Kudu saboda matsalolin shirye-shirye.

Shugaba Bola Tinubu ya amince da jirage biyar na Air Peace domin kwaso ‘yan Najeriya da suka nuna sha’awar dawowa gida.

Sama da mutum 1,000 sun nuna sha’awar dawowa Najeriya daga Afrika ta Kudu yayin da aka riga aka tantance mutum fiye da 500.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com