'Dan Afrika Zai Fafata da Turawa 5 a Zaben Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

'Dan Afrika Zai Fafata da Turawa 5 a Zaben Shugaban Majalisar Dinkin Duniya

  • 'Yan takara shida sun fuskanci tambayoyi na tsawon minti 90 a yayin da suke fafatawa a neman shugabancin Majalisar Dinkin Duniya
  • Tseren neman kujerar na gudana ba tare da wani fitaccen dan takara ba, yayin da ake son zabar sabon shugaban majalisar daga Janairun 2027
  • Za a fara kada kuri'ar farko a kwamitin sulhu a ranar 30 ga Yuli, kuma duk wanda ya yi nasara zai maye gurbin António Guterres

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

'Yan takara shida da ke neman kujerar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya sun fara gabatar da manufofinsu a wani taron tambayoyi da aka shirya domin bayyana hangen nesansu kan makomar kungiyar.

Taron, wanda zai gudana na tsawon minti 90 kuma Bloomberg ke watsawa kai tsaye, ya bai wa jami'an diflomasiyya, ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin fararen hula damar yi wa 'yan takarar tambayoyi kan shirinsu idan suka samu mukamin.

Kara karanta wannan

Shirin Amurka na samar wa Saudi nukiliya ya firgita 'yan Isra'ila

'Yan takarar shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Rahoton jaridar France 24 ya nuna cewa 'yan takarar da suke neman kujerar shugaban Majalisar Dinkin Duniya sun hada da:

  1. Michelle Bachelet ta Chile
  2. Maria Fernanda Espinosa ta Ecuador
  3. Rafael Grossi daga Argentina
  4. Rebeca Grynspan ta Costa Rica
  5. Carolyn Rodrigues-Birkett ta Guyana
  6. Macky Sall na Senegal

Rahoton ya nuna cewa dukkansu suna neman maye gurbin António Guterres, wanda wa'adinsa zai kare.

Shugabar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, Annalena Baerbock, ta ce taron wata dama ce ta musamman domin duniya ta fahimci ra'ayoyi da manufofin 'yan takarar.

Ta ce:

"A wannan duniya da ke kara fuskantar rarrabuwar kawuna, Majalisar Dinkin Duniya na bukatar shugaba mai kwarewa wanda zai sabunta kungiyar domin karni na 21, tare da kare kundin tsarin Majalisar Dinkin Duniya da ginshikanta uku."

Kalubalen da ke gaban sabon shugaba

Majalisar Dinkin Duniya na fuskantar matsananciyar matsalar kudi da kuma raguwar amincewar kasashe, musamman bayan gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta zargi kungiyar da almubazzaranci da kuma gazawa wajen cimma sakamako mai gamsarwa.

Kara karanta wannan

ADC: Ashiru Kudan ya zabi abokin takarar gwamna domin doke Uba Sani a Kaduna

Amurka na matsa lamba a mayar da hankali kan babban aikin kungiyar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, yayin da wasu kasashe ke dagewa cewa kare hakkin bil'adama da bunkasa ci gaba su ma muhimman ginshikai ne.

Sai dai masanin kungiyar International Crisis Group, Richard Gowan, ya ce wannan tseren bai samu armashi irin na shekarar 2016 ba, lokacin da aka zabi Guterres.

Ya kara da cewa yawancin 'yan takarar na kokarin kauce wa furta kalaman da za su iya bata wa Amurka ko sauran kasashen da ke da ikon yin fatali da sakamakon zabe rai.

Yadda za a zabi sabon shugaban MDD

Kafar labaran RFI ta rahoto cewa a ranar 30 ga Yuli ne mambobi 15 na Kwamitin Sulhu za su gudanar da kuri'ar farko cikin sirri domin bayyana wanda suka fi so.

Za a ci gaba da irin wadannan kuri'u har sai dan takara guda ya samu akalla kuri'u tara ba tare da wani daga cikin kasashe biyar masu ikon veto ya yi fatali da shi ba.

Bayan haka, za a mika sunan wanda aka zaba ga Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya domin tabbatar da nadinsa.

Ana sa ran sabon babban sakataren zai fara aiki daga ranar 1 ga Janairun shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com