Yaki da ta'addanci a Najeriya
Dandazon mutane da suka rasa gidajensu saboda matsalar tsaro a yankin karamar hukumar Bodinga ta jihar Sakkwato sun fito zanga-zanga don jawo hankalin gwamnati.
Hedkwatar rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun Amurka da aka turo aikin hadin gwiwa na nan daram, wadanda aka janye sun kammala aikinsu ne.
A labarin nan, za a ji cewa dakarun sojin Najeriya sun tari wasu tsagerun yan ta'adda da suka kai masu hari har sansaninsu da ke Bukuyyum a jihar Zamfara.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda 1,597, sun ceto mutum 1,516 da aka sace tare da gudanar da ayyukan tsaro sama da 14,000.
Sarakunan gargajiya 20 da sun tsere daga garuruwansu saboda hare-haren 'yan bindiga a Kwara, sun nemi taimakon rundunar tsaro ta Iru Ekun karkashin Sunday Igboho.
Rundunar sojin Najwriya ta samu galaba kan 'yan bindiga a wani samame ta sama da ta kai maboyarsu a jihar Neja, ta kuma lalata masu kayayyakin aiki.
Rundunar sojin Najeriya ta kama wasu mutane da suke kera bindigogi suna rabawa 'yan ta'adda a jihohin Arewa ta Yamma. An kama su da bindigogi biyar.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta tura dakaru zuwa yankin bayan samun labarin kashe almajirai da garkuwa da wasu yan gida daya a jihar Bauchi.
Rahotanni sun ce akalla sojoji 2 sun rasa rayukansu a hanyar zuwa kai dauki yayin da bam da tarwatse da motarsu a yankin karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari