Manyan Hanyoyin da Za a Bi a Iya Kawo Karshen Ayyukan Ta'addanci a Najeriya

Manyan Hanyoyin da Za a Bi a Iya Kawo Karshen Ayyukan Ta'addanci a Najeriya

  • Ministan tsaro da Gwamnan Kaduna sun bayyana cewa ingantaccen ilimi da hadin kan al’umma da jami’an tsaro na dakile ta’addanci da ‘yan bindiga
  • Sun yi wannan bayani ne yayin kaddamar da makarantar 'Kaduna Christian Academy' da abokan shugaban DSS suka gina domin Kiristoci a Kaduna
  • Shugabannin sun ce ilimi na taimakawa wajen yakar jahilci, talauci da tsattsauran ra’ayoyi da ke haddasa rashin tsaro a fadin kasar Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kaduna - Ministan tsaro, Christopher Musa, da Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, sun bayyana manyan hanyoyin da za a iya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Sun ce ingantaccen ilimi, kishin kasa da hadin kan al’umma da jami’an tsaro su ne manyan hanyoyin da za su taimaka wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun baza koma bayan an kama ɗan sandan ƙasar waje da bindiga a Katsina

Janar Christopher Musa da Gwamna Uba Sani sun nuna muhimmancin ilimi a yaki da ayyukan ta'addanci
Janar Christopher Musa (tsakiya) yayin kaddamar da makarantar Kaduna Christian Academy. Hoto: Ministry of Justice Kaduna
Source: Facebook

“Ilimi babban makami ne” - Janar Musa

Sun bayyana hakan ne yayin kaddamar da makarantar kiristoci ta Kaduna (KCA) wadda abokan Shugaban hukumar DSS, Oluwatosin Ajayi, suka gina in ji rahoton Channels TV.

Rahotanni sun nuna cewa watanni kadan da suka gabata, wadannan abokan ne suka taimaka wajen gina wata makarantar Islamiyya ga al’ummar Musulmi a Danbushiya da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, Christopher Musa ya bayyana makarantar a matsayin wata muhimmiyar hanya ta yaki da rashin tsaro ba tare da amfani da makamai ba.

Ya ce samar da zaman lafiya mai dorewa ya wuce amfani da sojoji da tattara bayanan sirri kadai. A cewarsa, ilimi na daga cikin manyan hanyoyin da za su taimaka wajen yakar jahilci da kuma tsattsauran ra’ayi.

“Idan aka ambaci tsaron kasa, mutane kan fi tunanin sojoji, jiragen yaki ko tattara bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano

“Amma gaskiyar ita ce, zaman lafiya mai dorewa yana dogara ne da yakar jahilci da kuma kawar da rashin makoma. Wannan makaranta makami ce ta koyarwa idan aka yi amfani da ita yadda ya dace."

- Christopher Musa.

Gwamnatin Kaduna ta yaba da aikin

Babban Lauyan jihar Kaduna kuma Kwamishinan shari’a, James Kanyip, wanda ya wakilci Gwamna Uba Sani a taron, ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar wajen fadada ilimi mai inganci.

Ya bayyana kaddamar da makarantar a matsayin wata alama ta fata, dama da sauyi ga al’umma masu zuwa, kamar yadda rahoton Punch ya bayyana.

Wakilin gwamnan ya ce:

“Ilimi na daga cikin manyan hanyoyin ci gaban mutum da al’umma baki daya. Duk makarantar da aka gina dama ce ta ilimi, kuma duk yaron da aka ilmantar yana kara karfin al’umma."
Janar Christopher Musa ya ce idan ilimi ya wadata, za a rage masu aikata ayyukan ta'addanci.
Ministan tsaro, Janar Christopher Musa yana jawabi a taron kaddamar da makarantar Kaduna Christian Academy. Hoto: Ministry of Justice Kaduna
Source: Facebook

CAN ta yi tsokaci kan matsalar tsaro

Shi ma Shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN na jihohin Arewa 19 da Abuja, Fasto Joseph Hayab, ya ce an kafa makarantar ne saboda muhimmancin ilimi wajen magance matsalolin tsaro, talauci da sauran kalubalen zamantakewa.

Ya bayyana cewa al’ummomi da dama har yanzu suna fama da matsalolin rashin makarantu masu kyau da kuma talauci wanda ke hana yara samun ilimi.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

A cewarsa, idan aka bai wa yara ilimi mai kyau, hakan zai rage yawan shiga ayyukan ta’addanci da miyagun laifuka a cikin al’umma.

Uba Sani ya gano cibiyar ayyukan ta'addanci

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya koka kan zargin garin Rijana da taimaka wa ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Sanata Uba Sani ya fito fili ya ayyana garin, wanda ke kan titin Kaduna zuwa Abuja, a matsayin cibiyar 'yan bindiga da ayyukan ta'addanci.

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya taba barazanar tada garin Rijana kan zargin taimakawa yan ta'adda da ke addabar jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com