'Muna Sakaci da Rashin Tsaro,' Dan Majalisar Wakilai Ya Yi Fallasa

'Muna Sakaci da Rashin Tsaro,' Dan Majalisar Wakilai Ya Yi Fallasa

  • Ɗan majalisar wakilai, Bamidele Salam, ya ce matsalar rashin tsaro na ci gaba ne saboda yawancin shugabanni ba sa fuskantar illolinta kai tsaye
  • Bamidele Salam ya bayyana cewa ’ya’yansu suna karatu a ƙasashen waje yayin da talakawa ke fama mafi girman matsalar hare-haren da ake kai wa
  • Salam, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo, ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a majalisa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo, Hon. Bamidele Salam ya yi magana kan rashin tsaro.

Hon. Salam ya ce shugabanni da dama suna yin watsi da matsalar rashin tsaro da ke ƙaruwa a ƙasar saboda ’ya’yansu suna zuwa makarantu masu zaman kansu ko kuma suna karatu a ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Lokuta 3 da Babachir Lawal ya canza gidan siyasa daga mulkin Buhari zuwa yau

Dan majalisar wakilai, Bamidele Salam
Bamidele Salam a zauren majalisar wakilai. Hoto: @bamidelesalamBS
Source: Twitter

'Ana watsi da tsaro,' Dan majalisa

Tribune ta wallafa cewa da yake jawabi a zaman majalisa ranar Laraba, a cikin wani bidiyo da ya bazu sosai, ɗan majalisar ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin kare makarantu a faɗin ƙasar.

Da ya ambaci wani karin magana na Yarbawa, Salam ya ce:

“Akwai wani karin magana a wajen Yarbawa cewa idan zaki ya shiga gari ya kashe ’ya’yan talakawa, wataƙila ba za a yi hayaniya ko jimami sosai ba. Amma ranar da zaki ya shiga gari ya kashe ɗan sarki, duk garin zai koma kamar makabarta.”

Ya kafa hujja da cewa masu riƙe da muƙaman gwamnati da dama ba sa jin raɗaɗin matsalolin da iyalai marasa ƙarfi ke fuskanta saboda ’ya’yansu suna makarantu masu zaman kansu, wasu ma suna karatu a wajen Najeriya.

“Saboda dalilan da muka sani, yawancin ’ya’yanmu da muke cikin shugabanci a yau suna zuwa makarantu masu zaman kansu. Wasu ma a wajen Najeriya saboda muna iya ɗaukar nauyin hakan.

Kara karanta wannan

PDP ta jijjiga, ƴan majalisar wakilai 6 sun yi mata tutsu, sun fice daga jam'iyyar

" Amma ’ya’yan talakawa, ma’aikata, malamai da masu sana’o’in hannu suna zuwa makarantun gwamnati, kuma ba za mu iya rufe ido kan haɗuran da ke fuskantar su da malamansu a yau ba,”

In ji shi.

Shawarar inganta tsaron Najeriya

Ɗan majalisar ya ba da shawarar kafa wata rundunar tsaro ta musamman da za ta mayar da hankali kan kare cibiyoyin ilimi a faɗin ƙasar.

“Kuma ina so in ba da shawarar cewa wani ɓangare na kudurin shi ne buƙatar gwamnatin tarayya ta kafa wata runduna ta musamman ko tsarin tsaro na musamman da aka tsara domin kare makarantu,”

In ji Salam.

Ya ce wasu ƙasashe da suka fuskanci irin waɗannan barazana sun samar da sabbin dabaru domin kare makarantu, yana mai ƙarawa da cewa a baya akwai tsarin tsaron makarantu a ƙarƙashin NSCDC, amma ba a samar masa da isasshen kuɗi ba.

'Yan majalisar wakilai
Lokacin da 'yan majalisar wakilai ke zama a Abuja. Hoto: Tajudeen Abbas
Source: UGC

Ga bayanin da ya yi a bidiyon da shafin GoldMyne TV ya wallafa a X:

Buratai ya magantu kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa tsohon hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai mai ritaya, ya daura alhakin ƙaruwar rashin tsaro kan wasu ’yan siyasa.

Kara karanta wannan

'Tinubu jan wuya ne a murde zabe': Babachir Lawal na ganin APC za ta zarce

Buratai ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi lokacin da yake mayar da martani kan sace ɗalibai da malamai a jihar Oyo.

A cewarsa, wasu ’yan siyasa sun shafe shekaru suna ɗaukar nauyi da tallafa wa miyagun mutane domin cimma manufofinsu na siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng