NiMet: Za a Shafe Kwana 3 ana Tsula Ruwa a Gombe, Kano da Sauran Jihohi

NiMet: Za a Shafe Kwana 3 ana Tsula Ruwa a Gombe, Kano da Sauran Jihohi

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen za a samu gajimare, hadari da ruwan sama a sassan Najeriya daga Laraba zuwa Juma'a
  • Jihohin Arewa, Tsakiyar Najeriya da Kudu za su fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a lokuta daban-daban cikin kwanaki ukun
  • NiMet ta gargadi jama'a da su yi taka-tsantsan saboda iska mai ƙarfi na iya gabatar da ruwan sama a wuraren da za a yi ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu gajimare, hadari da ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar daga ranar Laraba zuwa Juma'a.

Hukumar ta bayyana hakan ne a hasashen yanayin da ta fitar a Abuja ranar Laraba, inda ta ce wasu jihohin Arewa, Tsakiyar Najeriya da Kudancin ƙasar za su fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

Yadda aka yi ruwan sama
Lokacin da aka yi ruwan sama a Nafada, Gombe. Hoto: Aminu Ibrahim
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa NiMet ta kuma shawarci jama'a su kasance cikin shiri tare da bin sabbin bayanan yanayi domin kare rayuka da dukiyoyi.

Jihohin da za a yi ruwa

A cewar NiMet, a ranar Laraba za a samu hadari da ruwan sama a wasu sassan jihohin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara, Gombe, Bauchi, Taraba da Adamawa da safe.

Daga baya da rana ko yamma, ana sa ran hadari da ruwan sama za su bazu zuwa Kaduna da sauran jihohin Arewa maso Gabas.

A yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya kuwa, ana sa ran hadari da ruwan sama a Abuja, Filato, Nasarawa, Benue, Kogi, Kwara da Neja, yayin da yankunan Kudu za su samu ruwan sama a jihohin Ondo, Ekiti, Oyo, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.

Hasashen ranar Alhamis da Juma'a

NiMet ta ce ranar Alhamis ma za a ci gaba da samun hadari da ruwan sama a jihohin Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Kaduna, Taraba, Adamawa, Bauchi da Gombe.

Kara karanta wannan

Babban darakta a Kannywood Aminu Saira ya yi sabon aure, hotunan matansa sun jawo cece kuce

Haka kuma kusan dukkan yankunan Arewa ta Tsakiyar Najeriya za su samu hadari, yayin da yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu za su fuskanci ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi.

Ana ruwa a jihar Gombe
Lokacin da ake ruwan sama a jihar Gombe. Hoto: Ibrahim Abba Gombe
Source: Facebook

A ranar Juma'a kuwa, jihohin Borno, Yobe, Adamawa da Taraba za su fara samun hadari tun da safe, kafin ruwan saman ya bazu zuwa sauran jihohin Arewa daga baya.

NiMet ta yi gargadi ga jama'a

Hukumar ta gargadi cewa iska mai ƙarfi na iya gabatar da ruwan sama a wuraren da ake sa ran za a yi hadari.

Saboda haka, ta bukaci jama'a su ɗaure duk wani abu da iska za ta iya kwashewa, su guji tuki yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi, sannan su cire na'urorin lantarki daga wutar lantarki idan hadari ya tsananta.

NiMet ta kuma shawarci masu gudanar da zirga-zirgar jiragen sama da su rika neman bayanan yanayi na filayen jiragen sama domin sauƙaƙa tsara ayyukansu.

Maganar samar da abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa shirin Renewed Hope na uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ya kai tallafin kayan abinci jihar Ondo.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Shirin ya rabawa daruruwan marasa galihu da masu buƙata kayan abinci a Akure domin rage matsin tattalin arziki da kuma yaƙi da ƙarancin abinci.

Uwargidan shugaban ƙasar ta ce shirin na samun tallafi daga manyan masu bayar da gudummawa domin ci gaba da taimaka wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng