Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Yaudari Dattawa 50 yayin Zaman Sulhu a Jihar Zamfara

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Yaudari Dattawa 50 yayin Zaman Sulhu a Jihar Zamfara

  • Wasu dattawa 50 daga kauyen Magamin Diddi sun fada hannun ‘yan bindiga yayin wata tafiyar sulhu don tabbatar da zaman lafiya a Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani shugaban dabar ‘yan bindiga da ake kira Jammo ne ya yi garkuwa da su a dajin Muntsira
  • Haka zalika, bayanai sun nuna cewa an sako mutum 11 daga ciki, yayin da har yanzu mutum 39 ke hannun masu garkuwa da mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Akalla dattawa 50 daga kauyen Magamin Diddi da ke mazabar Magami/Faru a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun fada hannun ‘yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da dattawan ne bayan sun je tattaunawar sulhu da jagoran daya daga cikin dabar ‘yan bindiga mai suna Jammo.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi dabara sun cafke 'dan bindiga Kachalla Halilu da ya shiga kasuwa tsakar rana

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Jammo, wanda ake zargin shi ne shugaban dabar ‘yan bindigar da ke addabar dajin Muntsira a Maradun, ya gayyaci mutanen domin tattaunawar sulhu amma daga bisani ya yi garkuwa da su.

Ciyaman ya tabbatar da sace dattawa 50

Shugaban karamar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara, Hon. Bello Dosara, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

A cewarsa:

"Muna adawa da yin sulhu da ‘yan bindiga, haka ma Gwamna Dauda Lawal bai taba goyon bayan hakan ba. Amma mutanen yankin sun yanke shawarar ci gaba da tattaunawar ba tare da saninmu ba."

Dosara ya kara da cewa Jammo ya hana mutanen yankin zuwa kasuwa, amma gwamnati tana samar musu da kariyar jami'an tsaro domin su je kasuwa su dawo lafiya.

Shugaban karamar hukumar ya ce daga cikin mutanen da aka sace, an sako mutum 11 domin su sanar da jama'a abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

Dan Majalisa ya yi bayani

Dan majalisar mazabar Magami/Faru, Bello Husseini, ya ce kafin wannan lokaci Jammo ya yi arangama da rundunar tsaron jihar Zamfara ta Askarawa.

Ya bayyana cewa a lokacin an kashe biyu daga cikin manyan yaransa tare da kwace bindigoginsu, amma daga baya ya kashe askarawa biyu da sunan daukar fansa.

A cewar Husseini, Jammo ne ya nemi a yi sulhu bayan daya daga cikin yaransa ya mutu a wani farmakin sojoji da aka kai kauyen Kandare, in ji rahoton Daily Post.

Yadda aka yaudari dattawan

Duk da cewa gwamnati ba ta amince da hakan ba, al'ummar yankin sun kafa kwamitin mutum 50 da zai gana da shi, inda da isarsu wurin taron, Jammo ya karya alkawarinsa tare da yin garkuwa da su.

'Dan majalisar ya ce kwamandan ‘yan bindigar yana neman Naira miliyan 24 domin a mayar masa da bindigogi uku da aka kwace daga hannun yaransa.

"Mutanen da ya kama dattawa ne kuma babu wani dalili da zai sa ya yi garkuwa da su. Ya yaudare su ne bayan ya nuna cewa ya gaji da harkar ta'addanci kuma yana son sulhu," in ji shi.

Kara karanta wannan

An jibge yan sanda, sojoji da wasu dakaru a kewayen fadar shugaban kasa a Abuja

Dauda Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a wurin kaddamar da dakarun yaki da yan ta'adda Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Dosara da Husseini sun yi kira ga gwamnatin jihar Zamfara da jami'an tsaro da su kai farmaki dajin Natsira, wanda suka ce ya zama babbar mafakar ‘yan bindiga.

An kama hatsabibin dan bindiga a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun kama wani da ake zargin jagoran ‘yan ta’adda ne mai suna Kachalla Halilu a Zamfara.

Hakan ya biyo bayan bayanan sirrin da aka samu wanda ke nuna an ga dan bindigar a kasuwar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

An ruwaito cewa kayayyakin da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da babur, wayar hannu, hula da kuma magungunan dabbobi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262