Gwamna Ya Fadi Matakin da Zai Dauka da EFCC Ta Garkame Asusun Gwamnatin Jiharsa
- Gwamnatin Osun ta ce za ta maka EFCC a kotu bayan hukumar ta daskarar da asusun gwamnatin da ke bankin First Bank
- Antoni Janar na jihar ya ce EFCC ba ta da ikon daskarar da asusun gwamnati ba tare da umarnin kotu ba
- Gwamna Ademola Adeleke ya zargi EFCC da yunƙurin hana gwamnatin gudanar da ayyukanta gabanin zaɓen gwamna na Agusta 15
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta sanar da cewa za ta maka Hukumar EFCC a kotun tarayya bayan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta rufe asusun gwamnatin jihar.
Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari'a na jihar, Oluwole Jimi-Bada, ya ce ya samu umarni daga Gwamna Ademola Adeleke na fara shirin shigar da ƙara domin ƙalubalantar matakin.

Source: Twitter
"EFCC ba ta da ikon rufe asusun"
Ya bayyana cewa EFCC ta aika wa bankin First Bank wasiƙar "Post No Debit", wadda ta hana gudanar da mu'amala a asusun gwamnatin da ke bankin, in ji rahoton Punch.
Jimi-Bada ya ce hukumar na da damar binciken asusun gwamnati, amma ba ta da ikon daskarar da su ba tare da samun umarnin kotu ba.
Ya ce:
"Na samu umarni daga gwamna na garzaya Kotun Tarayya domin ƙalubalantar wannan mataki. EFCC na iya binciken asusun gwamnati, amma ba za ta iya daskarar da su ba tare da umarnin kotu ba."
Ya ƙara da cewa matakin na iya kawo cikas ga gudanar da harkokin gwamnati, amma gwamnatin za ta tabbatar an bi doka wajen warware rikicin.
Gwamnatin Osun ta musanta zargi
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Kuɗi na jihar, Sola Ogungbile, ya yi zargin cewa jami'an 'yan sanda sun kai samame babban reshen First Bank da ke Osogbo tare da kama wasu ma'aikatan bankin.

Source: Twitter
Gwamnatin Osun ta musanta zargin cewa ana amfani da kuɗaɗen gwamnati wajen yaƙin neman zaɓen Gwamna Ademola Adeleke.
The Cable ta rahoto cewa tun da farko, Adeleke ya yi iƙirarin cewa EFCC na shirin daskarar da dukkan asusun gwamnatin jihar da kuma na wasu manyan jami'an gwamnati.
An zargi EFCC da siyasantar da lamarin
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Kolapo Alimi, ya fitar, gwamnan ya ce idan wannan shiri gaskiya ne, to babban take doka ne.
A cewarsa, manufar daskarar da asusun gwamnatin ita ce kawo cikas ga ayyukan gwamnati gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.
Ya kuma jaddada cewa babu wata hujjar doka da ta ba EFCC damar daskarar da asusun gwamnatin jihar, yana mai cewa gwamnatin za ta bi duk hanyoyin shari'a domin kare haƙƙinta.
EFCC ta rufe asusun gwamnatin Osun
Tun da fari, mun ruwaito cewa, EFCC ta rufe wani asusun gwamnatin Osun wanda ake amfani da shi wajen biyan albashin ma'aikata kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna.
Gwamna Ademola Adeleke ya ce tun da farko ya yi gargaɗin cewa ana shirin daskarar da asusun gwamnati domin kawo cikas ga ayyukan gwamnati.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, EFCC ba ta fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, kuma ba a bayyana dalilin da ya sa aka ɗauki matakin ba.
Asali: Legit.ng


