Sojojin Najeriya Sun Rutsa 'Yan Ta'adda a Ƙungurmin Daji, An Saki Bidiyon Abin da Ya Faru

Sojojin Najeriya Sun Rutsa 'Yan Ta'adda a Ƙungurmin Daji, An Saki Bidiyon Abin da Ya Faru

  • Jiragen yaki na Rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 12 a wani harin sama da suka kai a Jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin sun kai harin ne kan wani sansanin ‘yan ta’adda da ke boye a yankin Chiralia
  • Rundunar ta ce wannan harin ya rage karfin ayyukan kungiyar ta’addanci a yankin, inda aka wallafa bidiyon abin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Akalla ‘yan ta’adda 12 ne aka kashe bayan sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai sun yi wa wani sansanin ‘yan ta’adda luguden wuta a Jihar Borno.

Bayanai sun nuna cewa sojojin sun far wa yan ta'addan ne bayan tattara sahihan bayanan sirri, lamarin da da ake ganin ya rage karfin ta'addanci a yankin.

Kara karanta wannan

Yadda za ku duba sunayen waɗanda hukumar Kwastam ta ɗauka aiki a 2026

Jirgin yaki.
Jirgin yaki na rundunar sojin saman Najeriya a bakin aiki Hoto: @airforcenig
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa an gudanar da harin ne a ranar 4 ga watan Agusta bayan samun sahihan bayanan sirri kan sake farfadowar ayyukan ‘yan ta’adda a yankin Chiralia.

An bayyana Chiralia a matsayin wani yanki mai cike da dazuzzuka wanda ‘yan ta’adda suka dade suna amfani da shi a matsayin mafaka saboda wahalar shiga yankin da kuma yadda ciyayi ke taimaka musu wajen boyewa.

Sojoji sun gano maboyar ‘yan ta’adda

Rahoton ya ce an tura na’urorin tattara bayanan sirri, sa ido da bincike (ISR) da misalin karfe 11:40 na safe domin gudanar da aikin leken asiri na musamman a yankin da ake zargi.

Zagazola ya ce:

“A yayin aikin, ma’aikatan sa ido sun gano wasu ‘yan ta’adda suna motsi a cikin sansanin, tare da wasu gine-gine a boyayyun wuraren rayuwa da aka rufe a karkashin ciyayi masu kauri.”

Ya ce an tantance wadannan wurare a matsayin maboyar aiki, cibiyoyin ajiye kayayyaki da kuma wuraren da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen shirya hare-hare.

Kara karanta wannan

An kashe dan siyasa da 'yan bindiga suka kai kazamin hari Filato da dare

An lalata sansanin gaba daya

Bayan tabbatar da wuraren da aka nufa, jiragen yakin sun kai jerin hare-haren sama na musamman kan wuraren da aka gano, inda suka yi nasarar afkawa gine-ginen da aka boye.

Rahoton ya ce binciken bayan harin (BDA) ya tabbatar da cewa an lalata sansanin yan ta'addan gaba daya, yayin da wuraren da suke buya suka koma kufai.

An kuma samu fashe-fashe da kuma ci gaba da kone-kone, lamarin da ya nuna lalacewar wasu kayayyaki da kayan aiki da aka ajiye a cikin sansanin.

Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Harin ya rage karfin ‘yan ta’adda

Rahoton ya nakalto majiyoyin soji suna cewa harin wani shiri ne da aka tsara bisa bayanan sirri, wanda ya nuna hadin gwiwa tsakanin na’urorin sa ido daga sama da kuma karfin kai hare-haren da jiragen yaki ke da shi.

Majiyoyin sun ce nasarar aikin za ta rage karfin kungiyar ta’addancin wajen samun mafaka, sake tsara hare-hare da kuma ci gaba da samun kayayyakin aiki a yankin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano inda aka boye gawar shugaban al'umma da aka hallaka a Imo

An kashe kwamandojin yan ta'adda a Borno

Kun ji cewa dakarun sojojin rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) sun kashe tarin 'yan ta'adda, ciki har da manyan kwamandojin da dama a Borno.

Aikin, wanda sashen dakarun saman na rundunar Operation Hadin Kai ya gudanar, ya farmaki sansanonin 'yan ta'adda da ke Metele, wani sanannen wurin buya na 'yan tawaye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262