Tinubu Ya Yunkuro da Karfi kan Tsaro, zai Murkushe 'Yan Ta'addan Najeriya

Tinubu Ya Yunkuro da Karfi kan Tsaro, zai Murkushe 'Yan Ta'addan Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ba za ta mika wuya ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuffuka da ke ƙoƙarin tsoratar da ƙasar ba
  • Ya sake jaddada alƙawarin gwamnatinsa na murƙushe masu tayar da hankali da kuma tabbatar da kuɓutar da dukkan ’yan Najeriya da ake tsare da su
  • Shugaba Tinubu ya kara da cewa yayin da ƙasar ke shirin tunkarar zaɓukan shekara mai zuwa, ya kamata ’yan Najeriya su guji tashin hankali kan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro da kuma tabbatar da kuɓutar da dukkan mutanen da ake tsare da su a faɗin ƙasar.

An bayyana matsayin shugaban ne a ranar Lahadi ta bakin Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, a wajen taron addu’ar a cibiyar Kiristoci ta kasa da ke Abuja, a wani ɓangare na bukukuwan ranar dimokuraɗiyya ta 2026.

Kara karanta wannan

Birtaniya za ta sa ido kan zaben Najeriya domin tabbatar da adalci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wajen wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bola Tinubu zai murkushe 'yan ta'adda

A wata sanarwa da mai taimaka wa SGF kan yaɗa labarai, Yomi Odunuga, ya fitar a X, Tinubu ya ce:

“Gwamnatin Najeriya ba za ta taɓa mika wuya ga ta’addanci, fashi da makami ko kowace irin barazanar masu aikata laifuffuka ba.”

Ya jaddada cewa kare rayuka ne babban abin da ya saka a gaba, yana mai cewa hare-hare da sace-sacen mutane da suka faru kwanan nan sun nuna cewa har yanzu akwai buƙatar ƙara ƙaimi da ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro.

Tinubu ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da dawowar dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya.

“Hare-hare da garkuwa da mutane da suka faru kwanan nan tunatarwa ce mai raɗaɗi cewa har yanzu akwai sauran aiki mai yawa da za a yi."
Sanata George Akume da Bola Tinubu
Sakataren gwamnatin tarayya, George Akume na gaisawa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Maganar Tinubu kan zaben 2027

Yayin da harkokin siyasa gabanin zaɓukan 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, shugaban ya buƙaci ’yan Najeriya su guji tashin hankali, kalaman ƙiyayya da furucin da ke haddasa rarrabuwar kawuna.

Kara karanta wannan

Mutanen Atiku sun koma APC, za su samawa Tinubu kuri'a miliyan 10

Punch ta wallafa cewa ya kuma gargadi matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen daba, yaɗa bayanan ƙarya ko tashin hankalin siyasa.

Tinubu ya kuma yi kira ga shugabannin addinai, sarakunan gargajiya, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin farar hula da su karfafa zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓe.

'Yan bindiga sun kai hari Abuja

A wani labarin, kun ji cewa wasu mahara ɗauke da makamai sun yi garkuwa da mutum huɗu tare da kashe wani ɗan sintiri a wani hari da suka kai birnin Abuja.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Aliyu ya ce harin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, yana mai cewa maharan sun zo da manyan makamai.

Ya kara da cewa kimanin mutum 28 ne suka kai harin, inda ya ce yana tsammanin sun yi sansani a yankin kafin su kai harin da ya kai ga sace fararen hula.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng