Janar Christopher Musa Ya Fadi Dabarar Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya
- Babban Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce Najeriya za ta shawo kan matsalar tsaro
- Sai dai ya ce ba haka kawai za a cimma wannan nasara ba, akwai rawar da jama'ar gari za su taka wajen dakile barazanar
- Janar Christopher Musa ya yabawa Rundunar Sojin Ruwa kan rawar da take takawa wajen yaƙi da ta'addanci da kare tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ƙasar za ta iya shawo kan matsalolin tsaro da ke addabarta.
Ministan ya bayyana cewa za a kai ga cimma wannan nasara ne idan al'umma suka haɗa kai tare da mara wa jami'an tsaro baya.

Source: Twitter
The Nation ta wallafa cewa Janar Christopher Musa ya bayyana haka ne a yammacin Alhamis, 4 ga watan Yuni, 2026.
Ya yi magana ne yayin bikin cika shekaru 70 da kafuwar Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, wanda aka gudanar a Eko Hotels and Suites da ke Legas.
Ministan tsaro ya bukaci taimakon jama'a
A ruwayar Vanguard, Janar Christopher Musa mai ritaya ya ce tabbatar da tsaro ba aikin jami'an tsaro kaɗai ba ne.
Ya bayyana cewa aiki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, yana mai kira ga 'yan ƙasa da su ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin a magance matsalar.
A cewarsa, Rundunar Sojin Ruwa ta taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun ƙasa, inda ta ke tallafa wa ayyukan tsaron cikin gida a sassa daban-daban na Najeriya.
Christopher Musa ya yabi rundunar sojin ruwa
Ministan ya yaba wa rundunar saboda kokarinta na kare hanyoyin jiragen ruwa, kayayyakin man fetur da iskar gas da ke cikin teku.

Kara karanta wannan
Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe

Source: Facebook
Haka kuma Christopher Musa ya jinjina yadda rundunar ke aiki wajen yaƙi da fashin teku da kamun kifi ba bisa ka'ida ba.
Ya ce waɗannan nasarori sun taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da ke inganta tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
Christopher Musa ya kuma jinjinawa haɗin gwiwar da Rundunar Sojin Ruwa ke yi da ƙasashen duniya da sauran abokan hulɗa.
Ya bayyana cewa hakan ya taimaka wajen ƙarfafa tsaro a yankin Tekun Guinea da sauran yankunan ruwa masu muhimmanci.
Janar Musa ya magantu kan rashin tsaro
A baya, kun samu labarin cewa Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya samo mafita kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a kasar nan.
Janar Christopher Musa ya bayyana cewa akwai matsalolin da ke rura wutar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita, kuma su ya kamata a magance domin a ji sauki.
Babban Ministan tsaron ya bukaci al'ummomin da ke bakin iyakokin kasar nan da su guji tallafawa ayyukan 'yan ta'adda, domin hakan ba zai haifar da 'da mai ido ba.
Asali: Legit.ng
