Tsohon Hadimin Buhari Ya Magantu kan Karuwar ’Yan Boko Haram a Mulkin Jonathan
- Bashir Ahmad ya bayyana damuwa game da ayyukan ta'addanci a Najeriya inda ya ba yan kasa shawara
- Matashin a ce bai taɓa ɗora wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan alhakin Boko Haram gaba ɗaya ba
- Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnati kaɗai ba za ta iya samar da tsaro ba sai da haɗin kan jama'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon mai taimaka wa marigayi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan harkokin yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya magantu kan rashin tsaro.
Bashir Ahmad ya bayyana cewa bai ɗora alhakin Boko Haram gaba ɗaya kan gwamnatin Goodluck Jonathan ba.

Source: Facebook
'Rashin tsaro nauyi ne kan kowa' - Bashir Ahmad
Ahmad ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce tun da dadewa yake ganin tsaron al’umma nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
Ya ce ko a lokacin da rikicin Boko Haram ya kai kololuwa, bai taɓa kallon gwamnati kaɗai a matsayin mai laifi ba saboda tsaro ya wuce abin da gwamnati za ta yi ita kaɗai.
A cewarsa, gwamnati na da alhakin samar da shugabanci, kayan aiki da dabarun tsaro, amma hakan ba ya nufin jama’a za su zura ido kawai.
Ya jaddada cewa dole ne al’umma, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da ɗaiɗaikun mutane su taka muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Source: Facebook
Rashin tsaro: Shawarar da Bashir Ahmad ya bayar
Bashir Ahmad ya ce samun zaman lafiya mai ɗorewa zai yiwu ne idan jama’a suna aiki tare da jami’an tsaro da shugabannin al’umma wajen hana aikata laifuka.
Ya ƙara da cewa masu aikata laifuka kan samu damar yin barna ne idan al’umma ba su bayar da haɗin kai ga hukumomin tsaro ba.
Saboda haka, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa yaƙi da masu laifi.
Ahmad ya ce:
“Tsaro nauyi ne na bai ɗaya wanda ke buƙatar cikakken haɗin kan kowane ɗan ƙasa domin kare al’umma da ƙasa baki ɗaya.”
Ya kuma jaddada cewa haɗin kai da ɗaukar alhaki tare ne kawai za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da tabbatar da makoma mafi aminci ga Najeriya.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan matsalar rashin tsaro, da rawar da shugabanni, jami’an tsaro da jama’a ke takawa wajen magance ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran laifukan tashin hankali a ƙasar.
Jonathan ya samu takara a PDP
Mun ba ku labarin cewa duk da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, an ayyana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa.
An tabbatar da takarar Jonathan ne a taron musamman da aka gudanar a Abuja, inda Fred Agbedi ya karbi takardar shaidar nasara a madadinsa.
Bayan jami’an tsaro sun hana shiga wurin taro na farko, shugabannin bangaren PDP sun sauya wuri tare da alkawarin sanar da ranar mika tuta.
Asali: Legit.ng
