Jami'an Tsaro Sun Baza Koma bayan an Kama Ɗan Sandan Ƙasar Waje da Bindiga a Katsina
- Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wani ɗan sandan Nijar a kan iyakar Jibiya da Magama a Katsina a wani yanayi da ya sa ya zama abin zargi
- An gano shi da makami yayin da aka kama shi, lamarin da ya kara jefa shakku a cikin aniyarsa na shigo wa cikin Najeriya
- An miƙa wanda ake zargin tare da makamin ga rundunar 'yan sandan Najeriya yayin da aka ci gaba da binciken lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina - Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) sun kama wani jami’in rundunar 'yan sandan ƙasar Nijar a mashigar iyakar Jibiya da Magama da ke ƙaramar hukumar Jibiya a jihar Katsina.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an kama mutumin ne da karfe 5:30 na yammacin ranar Juma’a, 5 ga watan Yuni, 2026 yayin gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a babbar ƙofar iyakar.

Source: Twitter
Majiyoyin sun shaida wa Zagazola Makama cewa jami’an kwastam sun tare mutumin ne domin tantance ko wane ne da kuma dalilin zuwansa wurin iyakar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
'Dan sandan kasar Nijar ya shigo Najeriya
Rahoton ya ce wanda ake zargin ya turje tare da tayar da hayaniya yayin da jami’an ke ƙoƙarin gudanar da aikinsu, lamarin da ya sa aka tsare shi domin ƙarin bincike.
Bayan da jami’an tsaro suka gudanar da bincike a jikinsa, sun gano bindiga kirar pistol tare da harsasai biyar masu girman milimita tara.
Majiyoyin sun bayyana cewa daga bisani an tabbatar da cewa mutumin jami’i ne na rundunar 'yan sandan ƙasar Nijar da ya shigo Najeriya.
An mika jami'in ƙasar Nijar ga ƴan sanda
Bayan kama shi, jami’an kwastam sun miƙa wanda ake zargin tare da bindigar da harsasan da aka samu a hannunsa ga hedikwatar rundunar 'yan sandan Najeriya da ke Jibiya.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano

Source: Facebook
Har yanzu hukumomin tsaro ba su bayyana cikakkun bayanai kan dalilin kasancewar jami’in ɗan sandan na Nijar a mashigar iyakar ba, ko kuma ko yana da izinin ɗauke da makamin da aka samu a hannunsa.
Haka kuma, ba a fitar da wata sanarwa a hukumance game da manufarsa ta zuwa yankin a lokacin da aka kama shi.
Majiyoyin tsaro sun ce bincike na ci gaba domin gano cikakken bayani kan lamarin da kuma tantance ko akwai wasu bayanai da suka shafi shigowarsa yankin da makamin.
Yan sanda sun yi kame a Katsina
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘yan sandan Katsina ta kama wani mutum da ake zargi da shiga asibitin Funtua domin neman mahaifar sabon jariri saboda tsafi.
Binciken ‘yan sanda ya nuna wanda ake zargin ya shiga harabar asibitin ne cikin yanayi mai tayar da hankali kafin a cafke shi kafin ya kai ga aikata mummunan aikin.
Rundunar ta gargadi jama’a kan shiga kowane irin nau'i na ayyukan tsafi da laifuffukan da ke barazana ga cibiyoyin lafiya da rayuwar al’umma da su kuka da kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
