Sojoji da Dama Sun Mutu da 'Yan Ta'adda Suka Bude Wuta ana Ruwan Sama a Borno

Sojoji da Dama Sun Mutu da 'Yan Ta'adda Suka Bude Wuta ana Ruwan Sama a Borno

  • 'Yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai mummunan hari kan sansanin sojoji da ke Mandara-Girau a karamar hukumar Biu ta jihar Borno
  • Rahoto ya nuna cewa 'yan ta'addan sun mamayi sojoji ana cikin ruwan sama mai karfi da safiyar yau Juma'a, inda suka kashe dakaru tara da raunata wasu
  • Wata majiya ta ce maharan sun zo ne da yawan gaske, lamarin da ya sa suka yi nasarar mamayar sojojin ba zato ba tsammani tare da jawo asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne sun kashe sojoji a wani sansanin soja da ke Mandara-Girau, a karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Mandara-Girau na da tazara kaɗan daga garin Biu, daya daga cikin manyan garuruwan yankin Kudancin jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu nasara kan 'yan ta'adda, an kashe tsageru da ceto mutanen da aka sace

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Boko Haram ta kai hari sansanin sojoji

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa maharan sun kai farmaki sansanin sojin ne da sanyin safiyar ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni, 2026.

An ruwaito cewa 'yan ta'addan sun bude wa dakarun sojojin wuta ba zato ba tsammani a yayin da ruwan sama mai karfi ke sauka.

Wata majiya ta ce maharan sun zo ne da yawan gaske, lamarin da ya sa suka yi nasarar mamayar sojojin ba zato ba tsammani tare da jawo asarar rayuka mai yawa.

An kashe sojoji tara, wasu sun jikkata

A cewar majiyar:

"Sun kashe dakarun sojoji tara tare da jikkata wasu da dama. An kuma datse kawunan wadanda aka kashe."

Majiyar ta kara da cewa 'yan ta'addan sun mamaye wani bangare na sansanin sojojin bayan harin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

An gano gawarwakin sojoji a bidiyo

A cikin wani faifan bidiyo mai tsawon minti daya da dakika 38 da aka fara yadawa a kafafen sada zumunta, an hangi gawarwakin sojoji takwas da aka rufe da barguna suna kwance a kasa.

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Gwamna Zulum.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum yana magana a taron Majalisar zartarwa Hoto: @ProfZulum
Source: Original

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin da yan ta'addan suka kai sansanin ba.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar hare-haren kungiyoyin masu tayar da kayar baya a wasu sassan jihar Borno da yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sojoji sun ceto wadanda aka sace

A sani labarin, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, a ƙarkashin aikin Operation Desert Sanity V/Siege Operation ta ragargaji 'yan ta'adda a Arewa mado Gabas.

Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda da dama tare daceto mutanen da aka yi garkuwa da su, kamar yadda jami'in yaɗa labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba ya tabbatar.

Uba ya bayyana cewa bayan gudanar da binciken lafiya na farko, an sake haɗa waɗanda aka ceton lafiya tare da iyalansu ta hanyar shugabancin al'ummar Ngoshe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262