Sarkin Musulmi Ya Fito Ya Yi Magana da aka Ce Ya Ce a Zabi Tinubu a 2027
- Fadar Sarkin Musulmi ta ce rahoton da ke ikirarin Muhammadu Sa'ad Abubakar ya bukaci a sake zaɓen Bola Tinubu a 2027 ba gaskiya ba ne
- Masarautar Sokoto ta jaddada cewa Sarkin Musulmi uba ne ga kowa, don haka ba zai goyi bayan wani ɗan takara ko jam'iyya ba
- Mai magana da yawun Sarkin Musulmi ya bukaci jama'a su yi watsi da rahoton tare da tabbatar da sahihancin labarai kafin yaɗa su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum
Jihar Sokoto – Tawagar yaɗa labarai ta Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ya bukaci 'yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Tawagar ta ce ba zai yiwu Sarkin Musulmi, a matsayinsa na uba ga dukkan 'yan Najeriya, ya fito ya goyi bayan wani ɗan takara ko ya shiga siyasar jam'iyya ba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Prince Bashir Adefaka ya sanya wa hannu a madadin tawagar yaɗa labaran Sarkin Musulmi a wani sako da suka wallafa a Facebook mai ɗauke da kwanan watan Talata, 4 ga Agusta, 2026.
"Sarkin Musulmi uba ne ga kowa"
Sanarwar ta bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da rahoton, tana mai bayyana shi a matsayin yunkuri na jawo sunan Sarkin Musulmi cikin siyasar jam'iyya domin biyan wasu muradu na kashin kai.
A cewar sanarwar:
"A sake bayyana cewa masarauta da kuma jagorancin addini da Sarkin Musulmi ke yi na matsayin uba ne ga kowa. Saboda haka, Mai Alfarma ba zai iya yin wani abu da ya sabawa wannan matsayi ba."
Ta kara da cewa Sarkin Musulmi na ci gaba da bai wa 'yan siyasa shawara, addu'a da jagoranci ba tare da la'akari da jam'iyyarsu ko akidarsu ta siyasa ba.

Source: Facebook
Magana kan labarun bogi
Tawagar ta jaddada cewa kofofin Sarkin Musulmi a bude suke ga kowa, kuma ba a taba nuna wariya ga duk wani ɗan Najeriya da ya nemi ganawa da shi ba.
Saboda haka, ta bukaci jama'a su yi watsi da duk wani yunkuri na danganta Sarkin Musulmi da yakin neman zaben wani ɗan takara kafin babban zaben shekarar 2027.
Haka kuma, sanarwar ta yi kira ga 'yan jarida da masu amfani da kafafen sada zumunta su rika tantance sahihancin labarai kafin wallafawa, domin kauce wa yaudarar jama'a da jefa manyan cibiyoyin gargajiya da addini cikin rigingimun siyasa.
'Tinubu ya cancanci yabo' Shettima
A wani labarin, mun ruwaito cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasar ya cancanci yabo ba suka ba.
Shettima ya bayyana hakan ne a taron tattalin arziki da zuba jari na jihar Delta, inda ya ce ajiyar kuɗin ƙasashen waje ta ƙaru daga dala biliyan 3 zuwa kusan dala biliyan 52 sakamakon manufofin gwamnatin Tinubu.
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, saboda goyon bayan da ya bai wa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng

