Jami'an Tsaro Sun Buga da Ƴan Bindiga da Suka Yi Yunkurin Garkuwa da Mutane a Kano
- Jami’an tsaron dararen hula, NSCDC sun fafata da wasu ƴan bindiga da suka yi yunkurin kai hari ƙaramar hukumar Kiru a jihar Kano
- Maharan sun jikkata wani makiyayi tare da sace ‘ya’yansa biyu kafin jami’an tsaro su fatattake su bayan an yi masu kiran gaggawa
- Jami'an hukumar NDC sun yi nasarar ceto yaran bayan an yi zazzafan dauki ba dade tare da nuna masu ƙarfin makami da kwarewar aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Jami’an hukumar tsaron fararen hula (NSCDC) reshen jihar Kano sun yi nasarar dakile wani yunkurin garkuwa da mutane tare da satar shanu.
Yan ta'addan sun yi yunkurin kai harin yankin Bakin Komau da ke Dangora a karamar hukumar Kiru inda suka jikkata bayin Allah.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Mai magana da yawun NSCDC a Kano, SC Ibrahim Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar hakan a ranar Juma’a 5 ga watan Yuni, 2026.
Ƴan bindiga sun kai hari Kano
A cewarsa, lamarin ya faru ne ranar Alhamis 4 ga watan Yuni, 2027 lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka kai hari kan wani makiyayi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun yi wa makiyayin munanan raunuka sannan suka yi awon gaba da ‘ya’yansa biyu tare da kokarin sace dabbobinsa.
Sanarwar ta ce bayan samun rahoton gaggawa, jami’an NSCDC da ke aiki a kusa da dajin Dansoshiya sun yi saurin isa wurin da abin ya faru domin ceto wadanda abin ya shafa.
Sanarwar ta ce:
“Da samun rahoton lamarin, jami’an NSCDC da ke bakin aiki a kusa da dajin Dansoshiya sun garzaya wurin tare da fafatawa da maharan a musayar wuta."
Hukumar ta bayyana cewa maharan sun kasa cimma manufarsu bayan da suka fuskanci zazzafan martani daga jami’an tsaron.
Kano: An ceto yara daga hannun ƴan bindiga
Kakakin hukumar ya tabbatar wa Legit cewa martanin ami’anta suka yi wa maharan, sun yi watsi da yaran da suka sace tare da tserewa cikin daji dauke da raunuka.

Source: Original
Kakakin hukumar ta ce:
“Bayan sun gaza shawo kan jami’an NSCDC, maharan sun bar yaran da suka sace tare da guduwa cikin daji, lamarin da ya hana su aiwatar da mugun nufinsu."
Hukumar ta ce mutanen da aka ceto sun hada da Abubakar Saleh mai shekaru 36 da Muhammad Inuwa Dille mai shekaru 30, kuma tuni aka hada su da iyalansu.
Haka kuma, makiyayin da aka kai wa hari, Alhaji Saleh mai shekaru 70, ya samu kulawar lafiya cikin gaggawa domin jinyar raunukan da ya samu.
NSCDC ta bayyana cewa an tura jami’anta yankin ne domin samar da tsaro ga aikin gina madatsar ruwa da ake yi a wurin, tare da kare wuraren kiwo da al’ummomin manoma daga ayyukan masu aikata laifuffuka.
Kwamandan NSCDC na jihar Kano, Mohammed Hassan Agalama, ya sake jaddada kudirin hukumar na ci gaba da kare rayuka, dukiyoyi da muhimman kadarorin kasa.
Ana kuka da rashin tsaro a Kano
A baya, mun wallafa cewa ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi kakkausar suka kan yadda ake tafiyar da harkokin tsaro a jihar.
Ya ce hare-haren da ake kai wa al’umma a wasu ƙananan hukumomi sun nuna cewa rayuka da dukiyoyin jama’a ba sa samun kariya yadda ya kamata, kuma ana kara kashe jama'a .
Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da suka addabi wasu yankunan jihar Kano.
Asali: Legit.ng

