'Yan Ta'adda Sun Yi Yunkurin Mamaye Sansanin Sojoji a Zamfara, An Yi Barin Wuta
- Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun fatattaki harin 'yan ta'adda kan sansanin soji a Kaura Namoda tare da ceto fararen hula tara da aka sace
- Jami'in soja guda da jami'in 'yan sanda guda sun rasu yayin musayar wuta, yayin da sojoji biyu suka jikkata kuma ake ci gaba da ba su kulawa
- Rundunar sojin ta musanta rahotannin da ke cewa jami'an tsaro shida sun mutu, tana mai tabbatar da cewa mutum biyu ne kawai suka rasa rayukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Zamfara - Dakarun Sector 2 na Operation FANSAN YAMMA sun dakile yunkurin da wasu 'yan ta'adda suka yi na kutse cikin Forward Operating Base (FOB) da ke Kasuwan Daji a ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta jihar Zamfara.
Rundunar ta kuma yi nasarar ceto fararen hula tara da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su yayin harin.

Source: Twitter
Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Zamfara
Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama'a na Rundunar Sojin Najeriya ta 8 Division da Sector 2 Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, in ji rahoton Vanguard.
Ya ce sojojin sun yi wa maharan luguden wuta mai ƙarfi, lamarin da ya tilasta musu tserewa bayan sun gamu da gagarumar turjiya.
Sanarwar ta ce harin ya faru da misalin ƙarfe 1:40 na safiyar ranar 2 ga Agustan 2026 lokacin da 'yan ta'addan suka yi ƙoƙarin kutsawa sansanin sojin a ƙarƙashin duhun dare.
Sai dai dakarun sun gano motsinsu cikin lokaci tare da buɗe musu wuta ta hanyar haɗin gwiwa, wanda ya tilasta musu janyewa cikin ruɗani.
Bayan dakile harin, ƙarin dakaru sun isa yankin tare da bin sahun 'yan ta'addan da ke guduwa. A yayin wannan samame ne aka yi nasarar ceto fararen hula tara da aka sace daga al'ummomin da ke kusa da sansanin.
Jami'an tsaro biyu sun rasu
Sai dai rundunar ta ce jami'in soja guda da jami'in 'yan sanda guda sun rasa rayukansu yayin musayar wutar.
Haka kuma, sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga, inda aka garzaya da su ta jirgin sama domin samun kulawar likitoci. Rundunar ta ce dukkansu suna cikin kwanciyar hankali.
Osoba ya bayyana cewa yanzu haka dakaru sun mamaye yankin gaba ɗaya, yayin da ake ci gaba da bincike domin tantance asarar da 'yan ta'addan suka yi tare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Source: Original
An yi watsi da rahotannin bogi
Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa jami'an tsaro shida sun mutu a harin.
A cewarsa, jami'in soja guda da jami'in 'yan sanda guda ne kawai suka rasa rayukansu, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya jaddada cewa Operation FANSAN YAMMA za ta ci gaba da kai hare-haren murƙushe 'yan ta'adda, kare al'ummomi masu rauni da kuma rusa cibiyoyin masu aikata laifuka har sai an dawo da cikakken zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma.
'Yan bindiga sun kashe sojoji
A wani labari, mun ruwaito cewa, ƴan bindiga sun kashe aƙalla sojoji shida tare da yin garkuwa da fiye da mutum 70 a Kasuwar Daji.
An ce maharan sun mamaye sansanin sojoji kafin su shiga garin da harbe-harbe, inda suka kashe mutane.
Wani tsohon mataimakin kakakin majalisa ya ce an kwashe kayan abinci da sauran dukiyoyi daga shaguna.
Asali: Legit.ng


