"Ku Daina Yi wa Fulani Kudin Goro," Peter Obi Ya Yi Jan Hankali kan Ayyukan 'Yan Bindiga
- 'Dan takarar shugababan kasa na NDC a zaben 2027 mai zuwa, Peter Obi ya soki yadda ake danganta manyan laifuffuka da wasu kabilu a Najeriya
- Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa ya sha fuskantar wariya saboda kasancewarsa dan kabilar Igbo
- Ya bukaci 'yan Najeriya su daina dora laifuffukan ta'addanci kan kabilar Fulani kadai, yana mai nuna cewa hakan bai dace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - 'Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya yi kira da a daina danganta aikata laifuffuka da wasu kabilu, yana mai cewa hakan na haifar da rabuwar kai a kasa.
Peter Obi ya yi wannan magana ne yayin da ake ci gaba da danganta ayyukan garkuwa da mutane da wasu laifuffuka da Fulani.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ya sha fuskantar hukunci da nuna wariya saboda kasancewarsa dan kabilar Igbo.
Peter Obi ya tuna abin da ya faru da shi
A cewarsa:
"A matsayina na inyamuri (Igbo) na sha fuskantar son zuciya, hukunci da lakabi saboda asalin kabilata."
Ya kara da cewa ba inyamurai kadai ke fuskantar irin wannan matsala ba, domin kusan dukkan kabilun Najeriya sun taba fuskantar irin wannan kalubale a wani lokaci.
Ya kare Fulani masu zaman lafiya
Tsohon gwamnan Anambra ya ce yana fahimtar irin radadin da Fulani masu son zaman lafiya ke ji idan aka yi musu kudin goro saboda ayyukan wasu tsirarun masu aikata ta'addanci a cikinsu.
Ya ce yawancin Fulani ba su da alaka da masu garkuwa da mutane ko ‘yan ta'adda da ake danganta wa kabilarsu.
Obi ya jaddada cewa laifi ba ya da kabila ko addini, yana mai cewa masu aikata miyagun laifuffuka ya kamata a dauke su a matsayin mutane daban, ba wakilan wata kabila ba.
"Barawo barawo ne, dan ta'adda dan ta'adda ne kuma mai garkuwa da mutane mai garkuwa da mutane ne. Ba wakilan wata al'umma ba ne," in ji Obi.
Peter Obi ya aika sako ga jami'an tsaro
Ya bukaci jami'an tsaro su gano masu laifi, su kama su kuma a hukunta su bisa doka, maimakon a zargi daukacin wata kabila da laifin wasu mutane kalilan.
Obi ya kuma yi nuni da yadda nuna wariya a Amurka ya haifar da fafutukar kare hakkin bil'adama, inda ya ambato kalaman Martin Luther King Jr. cewa ya kamata a rika hukunta mutum bisa halayensa, ba launin fatarsa ba.

Source: Facebook
Dan takarar shugaban kasar ya ce wajibi ne ‘yan Najeriya su rika alfahari da al'adunsu da gudunmawar da kabilunsu ke bayarwa, maimakon fadawa tarkon son zuciya.
Obi ya kammala da kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi adalci, mutunta juna da kuma fatan samun kyakkyawar makoma domin gina kasa mai hadin kai da ci gaba.
Peter Obi ya yi wa Kwankwaso tanadi
A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar shgaban kasa a NDC, Peter Obi ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso ba zai zama dan kallo ba idan suka kaf gwamnati a 2027.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta tsorata, ta ce Peter Obi zai iya ba Atiku mamaki a zaben 2027
Tsohon gwamnan ya ce shi da Kwankwaso za su yi aiki tare a matsayin abokan hulɗa masu cikakken iko wajen yanke muhimman shawarwari.
Obi ya ƙara da cewa za a rika tattaunawa da kowa kafin yanke manyan matakai, yana mai cewa hakan ne tsarin mulki mai kyau yake buƙata.
Asali: Legit.ng

