Sanata Mohammed Onawo Ya Fice daga Jam'iyyar ADC, Ya Fito Takarar Gwamna a Zaben 2027

Sanata Mohammed Onawo Ya Fice daga Jam'iyyar ADC, Ya Fito Takarar Gwamna a Zaben 2027

  • Sanata Mohammed Onawo ya sauya sheka daga jam'iyyar ADC zuwa APM yayin da ake shirye-shiryen babban zabe mai zuwa
  • Dan Majalisar dattawan ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa karkashin inuwar APM a 2027
  • Ya ce rikice-rikice da zargin magudi a zaɓen fidda gwani na ADC ne suka sa ya fice dga jam'iyyar hadaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa, Nigeria - Sanata Mohammed Onawo, mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya fice daga jam’iyyar hadaka ta ADC) zuwa APM.

Sanatan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a Lafia yau Laraba, inda kuma ya sanar da aniyarsa ta neman kujerar gwamnan Jihar Nasarawa a zaɓen 2027.

Sanata Mohammed Onawo
Sanata Mohammed Onawo lokacin da ya kai ziyara ofishin APM da ke jihar Nasarawa Hoto: APM Nigeria
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Sanata Mohammed Onawo ya samu nasara ne ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, kafin daga baya ya fice daga PDP ya koma ADC.

Kara karanta wannan

Adeleke ya zargi EFCC da shirin yi wa gwamnatinsa illa gabanin zaɓen Osun

Dalilin ficewar Sanata Mohammed daga ADC

Onawo ya ce ya koma APM ne saboda zargin karkatar da tsari da rashin bin tsarin dimokuraɗiyya a zaɓen fidda gwani na takarar gwamna da ADC ta gudanar a jihar.

Ya ce sauya shekar tasa ta biyo bayan tuntubar manyan dattawan siyasa, abokan hulɗarsa da kuma masu ruwa da tsaki a faɗin jihar.

“Wannan mataki ya samo asali ne daga buƙatar samun sabuwar kafa wadda ta dace da hangen nesa na, bunƙasa al’umma daga tushe da kuma haɗin kan Jihar Nasarawa,” in ji shi.

Sanatan ya bayyana zaɓen fidda gwani na ADC a matsayin “abin kunya”, yana mai cewa ya fi abin da ya sa shi barin PDP muni.

Ya ayyana neman takarar gwamna

Mohammed Onawo ya ce ya yi wa al’ummar jihar hidima yadda ya kamata a Majalisar Dattawa, kuma lokaci ya yi da zai ɗaga wannan hidima zuwa wani matsayi mafi girma.

Kara karanta wannan

Musulma mai suna Rashida ta lashe zabe a kasar Amurka

“Bayan tuntuba mai zurfi, na yanke shawarar komawa APM tare da amsa kiran tsayawa takarar gwamnan Jihar Nasarawa a 2027,” in ji shi.

Ya bayyana cewa Nasarawa na buƙatar shugaba wanda ya fahimci bambancin al’ummarta, yana mai alkawarin haɗa kan kabilu da addinai daban-daban idan aka zaɓe shi.

Sanata Mohammed Onawo.
Sanata Mohammed Onawo tare da wasu shugabannin jam'iyyar APM reshen jihar Nasarawa Hoto: APM Nigeria
Source: Facebook

Sanatan ya ce gogewarsa a siyasa, ƙwarewar majalisa da kuma kyakkyawar alaƙarsa da jama’a sun sanya shi a gaba idan aka kwatanta da sauran masu neman kujerar gwamna, cewar rahoton Punch.

Gwamnan Nasarawa ya zaɓi magajinsa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana dalilin zaban Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin magajinsa a zaben 2027.

Gwamna ya ce ya duba cancantar wanda ya zaba ne domin samun saukin cin zabe ba tare da wata matsala ba.

Gwamna Sule ya bayyana cewa da yawa daga cikin masu neman takara sun cancanta amma dole ya duba mafi saukin samun nasara a cikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262