Rahoto daga Isra'ila Ya Tona Asirin Yadda Trump Ya Shiga Tsaka Mai Wuya kan Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce za a bude mashigar ruwa ta Hormuz nan ba da jimawa ba, ko kuma Iran za ta fuskanci sabon mummunan hari
- Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun yi ikirarin cewa Trump da masu ba shi shawara na neman cimma yarjejeniya da Iran "ko ta halin ƙaƙa"
- Iran ta musanta cewa tana tattaunawa kai tsaye da Amurka, tana mai cewa tana aiki tare da Oman kan hanyoyin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington DC, Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yin barazana ga Iran, inda ya ce idan ba a sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz cikin gaggawa ba, Amurka za ta kai wani sabon hari mai tsanani.
Trump ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi, inda ya ce ana ci gaba da tattaunawa mai kyau da Iran, amma ya yi gargadin cewa idan Tehran ta janye daga alkawurranta, Amurka za ta koma kai hare-hare.

Source: Getty Images
Al Jazeera ta rahoto cewa wasu kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ambato wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa Trump da masu ba shi shawara na neman cimma yarjejeniya da Iran "ko ta halin ƙaƙa."
Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa Isra'ila ba ta samun bayanai kan yadda ake tattaunawa kai tsaye tsakanin Amurka da Iran a halin yanzu.
Trump ya sake yi wa Iran barazana
Trump ya ce yana fatan warware rikicin ta hanyar diflomasiyya maimakon yaƙi, amma ya jaddada cewa idan Iran ta karya yarjejeniyar da ake tattaunawa a kanta, ba zai yi ƙasa a gwiwa wajen kai sabon hari ba.
Ya ce:
"Za a buɗe mashigar Hormuz nan ba da jimawa ba, ko kuma za su sha mummunan hari. Idan suka sake janyewa, za a kai musu hari mai tsanani. Sun san haka."
Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa hare-haren da aka kai wa Iran a baya sun yi tasiri sosai, amma har yanzu yana fatan ba za a sake komawa amfani da ƙarfi ba idan aka cimma matsaya ta hanyar tattaunawa.

Kara karanta wannan
Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta sake tayar da sabon tarnaki bayan ikirarin Trump
Iran ta bayyana matsayarta
Sai dai CNN ta rahoto cewa gwamnatin Iran ta musanta ikirarin cewa tana tattaunawa kai tsaye da Amurka.
Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya ruwaito cewa kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce ƙasarsa na aiki tare da Oman wajen tsara hanyoyin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci a mashigar Hormuz.

Source: Getty Images
A nasa bangaren, Qatar ta bukaci a tabbatar da 'yancin zirga-zirga a mashigar Hormuz bisa dokokin ƙasa da ƙasa, tare da jaddada cewa duk wata sabuwar yarjejeniya ta kasance bisa amincewar ƙasashen yankin.
Iran ta soke harin Ukraine
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani babban mai ba Jagoran Addinin Iran shawara, Mohsen Rezaei, ya yi ikirarin cewa Iran ta shirya kai hari kan wurare uku a Ukraine kafin daga bisani ta soke shirin.
A cewarsa, an dakatar da harin ne bayan Ukraine ta nemi afuwa kan harin da ta kai wa wani jirgin ruwa da ke ɗauke da kayan aikin soja tsakanin Iran da Rasha.
Sai dai Rezaei bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da ikirarinsa ba, kuma ba a samu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan batu ba.
Asali: Legit.ng
