Ba Shari'ar Musulunci: Ƴan Bindiga da Suka Sace Ɗalibai a Oyo Sun Fadi Bukatunsu

Ba Shari'ar Musulunci: Ƴan Bindiga da Suka Sace Ɗalibai a Oyo Sun Fadi Bukatunsu

  • Shugabar makarantar da aka sace a Oyo ta ce masu garkuwar ba sa neman Naira biliyan ɗaya kamar yadda ake fada a baya
  • Haka kuma ta yi magana a kan cewa 'yan bindigan sun nemi lallai sai an kafa tsarin Shari'ar Musulunci a Najeriya
  • Ta bayyana cewa ainihin abin da masu garkuwa da mutanen suka ce suna bukatar a yi masu kafin a sako dalibai da makaman da aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo – Wani sabon faifan bidiyo na mutanen da aka sace daga makarantun jihar Oyo ya bayyana inda aka ji ainihin bukatar 'yan bindigan.

Rachael Alamu, shugabar makarantar da ke Ahoro-Esinle a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, ta ƙaryata cewaa masu garkuwa da su sun nemu N1bn.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Abubuwa 4 da 'yan ta'adda suka nema kafin su sako dalibai da malaman Oyo

An gano ainihin bukatar yan bindiga da suka sace daliban Oyo
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta wallafa cewa haka kuma ta roki jama'a da su yi watsi da maganar da ake cewa 'yan bindigan sun nemu a kafa tsarin Shari'ar Musulunci a Najeriya.

Bukatar masu garkuwa da 'yan makarantun Oyo

Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa Alamu da ke cikin waɗanda aka sace tare da ɗalibai da malamai, ta ce masu garkuwar sun bayyana masu bukatunsu.

Ta ce sun bayyana masu cewa abin da suke nema kawai shi ne a saki wasu daga cikin 'yan ta'addan da hukumomi ke tsare da su.

Daya daga cikin wadanda aka sace ta ce ba a taba tilasta masu ibadar Musulunci ba
Taswirar jihar Oyo inda aka sace dalibai da malamansu Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cikin bidiyon da aka fitar ranar Litinin, 8 ga watan Yuni, 2026, shugabar makarantar ta ce wasu bayanan da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai sun ƙara dagula halin da waɗanda aka sace suke ciki.

Ta ce ranar da aka fitar da bidiyon ta cika kwana 24 da kasancewarsu a hannun masu garkuwar, inda ta roƙi 'yan Najeriya da su taimaka wajen yaɗa gaskiyar abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo

Halin da 'yan makarantun Oyo ke ciki

Alamu ta ce tun bayan da aka sace su, masu garkuwar ba su tilasta masu yin ibadar addinin Musulunci ba.

Ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa masu garkuwar suna neman kuɗi, makamai ko kafa tsarin Shari'ar Musulunci ba gaskiya ba ne.

A cewarta:

"Abin da suke nema kawai shi ne a saki wasu daga cikin mutanensu."

Ta kuma yi kira ga jama'a da kada su bari gwamnati ko wasu su yaudari duniya da bayanan da ba su dace da abin da ke faruwa ba.

An zargi gwamna da shirya sace daliban Oyo

A baya, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi zargin cewa an shirya sace ɗalibai da malamai a wasu makarantun jihar Oyo ne da gan-gan.

Ya yi zargin cewa gwamnatin Gwamna Seyi Makinde ce ta shirya sace su a matsayin wani yunƙuri na ƙoƙarin bata sunan shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ayo Fayose ya ce ba a yin adalci wajen zargin shugaban kasa da matsalolin tsaro, alhali gwamnatocin jihohi ya kamata a rika jefa wa tambayoyi a kan tsaron jama'arsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng