Lamari Ya Munana, Malamin Addini Ya Taso Tinubu a Gaba Ya Yi Murabus kan Tsaro
- Rashin tsaro a fadin Najeriya ya fara daukar sabon salo wanda ya jawo manyan mutane da malaman addini ke korafi a kai
- Fasto Johnson Suleman ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki mataki mai tsauri kan masu daukar nauyin ta’addanci a Najeriya
- Ya ce matsalar tsaro ba za ta kare ba idan gwamnati ta ci gaba da kama masu kai hare-hare kawai ba tare da bin wadanda ke daukar nauyi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Cocin Omega Fire Ministries International, Fasto Johnson Suleman, ya fusata game da tabarbarewar matsalar tsaro.
Fasto Suleman ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki matakin gaggawa kan masu daukar nauyin ta’addanci da laifuffukan tashin hankali a fadin Najeriya.

Source: Twitter
An shawarci Tinubu kan rashin tsaro

Kara karanta wannan
Satar dalibai: Hanyoyi 6 da makarantu za su bi su kare kansu daga 'yan bindiga a Najeriya
Da yake magana yayin wani taron ibada a coci, Suleman ya ce matsalar tsaro a kasar ba za a warware ta ba idan aka mai da hankali kawai kan wadanda ke kai hare-hare, cewar Tribune.
A cewarsa, babban kalubalen shi ne mutanen da ke bayar da kudi, makamai da tallafin sufuri da ke taimaka wa ta’addanci ya ci gaba.
Ya jaddada cewa gano, kama da gurfanar da masu daukar nauyin ta’addanci shi ne hanya tilo da za ta kawo karshen kashe-kashe, satar mutane da ayyukan ‘yan bindiga a sassa da dama na kasar.
Ya ce:
“Masu daukar nauyin ta’addanci su ne babbar matsalarmu. Ku kama su. Idan Shugaban kasa ba zai iya shawo kansu ba, ya kamata ya sauka ya bar wani ya yi.”

Source: Facebook
'Musabbabin shigar matasa ta'addanci'
Fasto Suleman ya kara da cewa yawancin matasan da ke shiga ayyukan tashin hankali yanzu sakamakon tsofaffin hanyoyin ta’addanci ne da aka bari suka yi karfi tsawon shekaru.
Limamin ya ce kama masu kai hare-hare ba tare da rushe hanyoyin da ke bayan su ba ba zai kawo zaman lafiya mai dorewa ba.
Duk da sukar da ya yi wa gwamnatin kan yadda take tafiyar da matsalar tsaro, Suleman ya yaba wa hukumomin tsaron Najeriya, yana bayyana Sojojin Najeriya, ‘yan sanda da DSS a matsayin wasu daga cikin mafi kwarewa a duniya.
Ya ce jami’an tsaron Najeriya suna da kwarewa da ilimi daga kasashen waje, amma suna bukatar karin goyon baya domin su iya tunkarar masu tayar da hankali yadda ya kamata, cewar Daily Post.
Ya kara da cewa:
“Wadanda kuke fuskanta yanzu ‘ya’yan wadancan ‘yan ta’adda ne da aka shigo da su suna da shekaru shida a 2014, yanzu sun kai 19 ko 21. Shi ya sa kuke ganin yara suna dauke da bindigar AK-47. Ku kama masu daukar nauyin da ke basu karfi."
Fasto ya caccaki Bola Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Fasto Johnson Suleman ya danganta matsalolin tattalin arzikin Najeriya da zaben 2023, yana cewa rashin kyakkyawan zabi ya jawo haka.
Johnson Suleman ya yi kakkausar suka kan manufofin gwamnatin Bola Tinubu, musamman kan yadda aka tafiyar da bangaren man fetur.
Ya ce manufofin Tinubu sun jefa Najeriya cikin mummunan hali, yana mai jan hankalin kan daukar tsauraran matakai.
Asali: Legit.ng
