An Kama Tarin Magungunan Rage Radadi da ake Shirin Kkai wa Boko Haram

An Kama Tarin Magungunan Rage Radadi da ake Shirin Kkai wa Boko Haram

  • Jami'an DSS da masu gadin dazuka sun kama tarin kayan magunguna da ake zargin an nufi mika su ga mayakan ISWAP a jihar Borno
  • Kayan da aka kwato sun hada da magungunan rage radadi, magungunan kashe kwayoyin cuta, alluran maganin zazzabin cizon sauro
  • Majiyoyin tsaro sun ce kayan na da alaka da yunkurin tallafawa mayakan ISWAP bayan ragargazarsu da sojoji suka yi suka masu raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Jami'an hukumar DSS da masu gadin dazuka sun kama magunguna da ake zargin wasu mutane za su mika su ga mayakan ISWAP da suka jikkata a Borno

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a jihar Borno, tare da hadin gwiwar masu gadin dazuka ne suka kama magungunan.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Abubuwa 4 da 'yan bindiga suka nema kafin su sako dalibai da malaman Oyo

Mutanen da aka kama a Borno
Wadanda aka kama bisa zargin taimakon Boko Haram da magani. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa ana zargin an nufi mika su ga mayakan kungiyar ISWAP bayan wani farmaki da aka kai masu Arewa maso Gabas.

Yaushe aka kama magungunan?

Majiyoyin tsaro sun ce an tare kayan ne a ranar Juma’a a karamar hukumar Kaga yayin wani aikin hadin gwiwa da aka gudanar a wata hanya da ake zargin masu samar da kayan ga ‘yan ta’adda ke amfani da ita a cikin dazuka a jihar.

A cewar majiyoyin, kayayyakin da aka kama sun hada da dimbin magungunan rage radadi, alluran maganin zazzabin cizon sauro.

Haka zalika akwai magungunan kashe kwayoyin cuta da sauran su, tare da wasu kayan masarufi da ake kyautata zaton suna cikin kayan 'yan ta'addan.

Majiyoyin sun kuma nuna cewa kayan suna da alaka da yunkurin sake samar da kayayyaki ga mayakan ISWAP da aka ce sun yi asara mai yawa.

Rundunar ta ce 'yan ta'addan fuskantar tangarda bayan wasu hare-haren da aka kai bisa bayanan sirri da suka hada da rundunar sojin Amurka da jami’an tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi dabara sun cafke 'dan bindiga Kachalla Halilu da ya shiga kasuwa tsakar rana

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Sojoji na cigaba da kai farmaki

Rahoton jaridar the Cable ya nuna cewa sojojin sun bayyana kamen a matsayin wani bangare na kara kaimi wajen tarwatsa hanyoyin samar da kayayyaki ga ‘yan ta’adda.

Sun ce za a cigaba da farautar masu taimakon 'yan ta'adda, musamman wadanda ke taimakawa wajen kai magunguna da sauran kayan tallafi zuwa maboyarsu da ke wurare masu nisa.

An tattaro cewa binciken farko ya nuna ana jigilar kayan ne kadan-kadan domin kauce wa ganowa daga jami’an tsaro da ke sintiri a hanyoyi.

Tun daga lokacin da aka kama kayan, an kwace su domin gudanar da bincike a kansu, yayin da hukumomin tsaro suka kaddamar da wani shiri na kamo karin masu taimakawa ‘yan ta’adda.

Jami'an Sojoji sun cafke Kachalla Halilu

A wani labarin mun kawo muku cewa dakarun Najeriya sun yi kwanton bauna sun kama dan bindigan da ake nema ido rufe a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun buga da ƴan bindiga da suka yi yunkurin garkuwa da mutane a Kano

Rahotanni sun nuna cewa an cafke Kachalla Halilu ne yayin da ya shiga kasuwa a karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.

Sojojin Najeriya sun ce sun kama dan ta'addan tare da wasu kayayyaki da suka hada da babur, kuma za su cigaba da kai farmaki kan 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng