Ndume: Sanata Ya Faɗi Wurin da Ya Dace Amurka Ta Kafa Sansanin Soji a Jihar Borno

Ndume: Sanata Ya Faɗi Wurin da Ya Dace Amurka Ta Kafa Sansanin Soji a Jihar Borno

  • Sanata Ali Ndume ya nemi agajin Amurka a kan ta kafa sansanin soji a tsaunukan waɗansu daga cikin sassan jihar Borno
  • Ya ce hakan zai taimaka wajen fatattakar mayaƙan Boko Haram daga wasu daga cikin tsaunuka da manyan daukan da ke jihar
  • Ndume ya jaddada cewa rundunar sojin Najeriya na bukatar ƙarin kayan aiki da goyon baya domin yaƙi da ta'addancin da ya addabi jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno –Tsohon bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, ya bayyana goyon bayansa ga ƙarin kasancewar sojojin Amurka a jihar Borno, inda ya bukaci ƙasar ta kafa sansanin soji a tsaunukan Mandara.

Ya bayyana cewa daukan wannan mataki zai taimaka matuka wajen kawar da mayaƙan Boko Haram da ke aiki a yankin da kuma kawo harin da suke yi daga can.

Kara karanta wannan

Auren gata: Abin da Hisbah za ta yi wa maza da mata 3,000 a Kano kafin a biya sadaki

Ndume ya nemi ɗauki Amurka a Borno
Sanata Ali Ndume yana jawabi a Majalisar Dattawa Hoto: Senator Ali Muhammad Ndume
Source: Facebook

Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yi wannan kira ne yayin wata hira da tashar Channels Television a shirin Politics Today ranar Lahadi, 7 ga watan Yuni, 2026.

Ndume ya nemi ɗauki Amurka

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ndume ya bayyana cewa Amurka na da fasaha da kayan aikin da za su iya taimakawa wajen lalata sansanonin 'yan ta'adda da ke tsaunukan Mandara, dajin Sambisa da sauran wurare.

Sanatan ya ce zai yi matuƙar farin ciki idan Amurka ta kafa sansaninta a yankin Gwoza da ke kusa da tsaunukan Mandara domin korar mayaƙan Boko Haram daga yankin baki ɗaya.

A cewarsa, tsaunukan Mandara na da muhimmiyar matsayi ta fuskar tsaro saboda daga can za a iya sa ido kan dajin Sambisa da sauran wuraren da 'yan ta'adda ke amfani da su.

Ndume ya bayyana cewa fasahar sa ido ta Amurka za ta taimaka wajen gano motsin mayaƙan Boko Haram tare da dakile ayyukansu cikin sauri.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta yi magana kan sace Janar da matarsa, ta fadi kokarin da take yi

Ndume ya yi magana kan ƴan ta'adda

Sanatan ya kuma ce yanayin ƙasar Borno ya ba wa 'yan ta'adda damar amfani da hanyoyi daban-daban wajen zirga-zirga da samun kayan tallafi.

A cewarsa, idan aka katse waɗannan hanyoyi daga Sambisa zuwa Tafkin Chadi da sauran yankunan da mayaƙan ke amfani da su, za a rage yawan hare-haren ta'addanci sosai.

Senator Ali Ndume ya ce Amurka za ta taimaka wa jami'an tsaro
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa hakan ba zai yiwu ba sai an samar da isassun jami'an tsaro da kayan aiki a ƙasa, yana mai jaddada cewa rundunar sojin Najeriya na bukatar ƙarin tallafi da kayan aiki.

Kalaman Ndume na zuwa ne yayin da Najeriya da Amurka ke ci gaba da haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta'addanci a Arewa maso Gabas.

Borno: Sojoji sun fatattaki ƴan ta'adda

A baya, mun kawo labarin cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutanen da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar Borno.

Sojojin sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza da ke Borno.

Dakarun sojojin sun ba da kulawa ta hanyar duba lafiyar mutanen da aka yi nasarar ceto wa kafin mika su ga iyalansu da suka dade cikin jimamin rashinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng