Gwamnatin tarayyar Najeriya
Wani mamba a jihar Sakkwato ya ware zunzurutun kudi N200m don tallafawa Almajirai, marasa karfi da mata a yankinsa. Mamban tuni ya fara rabawa Almajirai babura.
Wani dan wasan kwallon kafan kulob Kano Pillars ya bata daga tafiya hutun kwanaki hudu. Dan wasan makwanni biyu kenan ba a ji labarin inda yake ba ko alamarsa.
Rundunar 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wa sojojin Najeriya hari a wani yankin jihar jihar Yobe. A harin kashe sojoji 13 an kuma raunata da yawa daga cikinsu.
Wata babban kotunmajistare ta bada belin dan gwagwarmaya Sowore a kan kudi Naira miliyan 20. Kotun ta bada belin ne kafin sauraran yanke hukunci a nan gaba.
Kwayar cutar korona ta hallaka mutane sama da 1,300 a Najeriya yayin da sama 100,000 ne suka kamu. Cutar ta harbi, mutane 1024 a ranar lahadi 10 ga Janairu.
Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa babu wani abu mai cutarwa cikin rigakafin korona balle kuma wani microchip. Ta bayyana ba wanda zai cutu.
Gwamnan jihar Ondo ya bukaci gwamnati ta karfafa samar 'yan sandan jihohi domin inganta tsaro da kawar da ta'addanci a Najeriya. Ya kuma yaba da aikin sojoji.
Rikici ya barke a jihar Oyo bayan da 'yan kungkyar Amotekun suka sheqe wani bafulatani da 'ya'yansa biyu. Kisan gillan ya faru ne jiya asabar a yankin fulanin.
Sojojin Najeriya sun samu nasarar afkawa 'yan bindiga a jihar Zamfara. Sun kashe 'yan ta'adda sama da 50 sun kuma kwato dabbobi a hannunsu sama da 300 a harin.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari